Daga Rabon Kayan Azumi, Kanawa Sun Dura kan 'Dan Majalisa, Sun Ragargaje Shi
- 'Dan majalisar Tarauni, Muktar Yarima, ya raba dawa da gero ga jama’arsa a matsayin tallafin Ramadan, abin da ya haddasa cece-kuce
- Mazauna yankin sun caccaki dan majalisar a shafukan sada zumunta, suna masu cewa su ba 'ya'yan dokuna ba ne da za su ci dawa da gero
- Wasu sun bar kayan tallafin da aka basu a wurin rabawa, yayin da magoya bayan Yarima ke cewa an kuma raba shinkafa da wake ga jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tarauni a jihar Kano, Muktar Yarima, ya raba dawa da gero a matsayin tallafin azumin Ramadan ga 'yan mazabarsa.
Sai dai, tun bayan gabatar da shirin rabon hatsin ne dan majalisar ke fuskantar suka daga 'yan mazabar tasa, inda kafofin sada zumunta suka cika da sukarsa.

Source: Facebook
Kano: An soki dan majalisa kan raba gero, dawa
Wasu mazauna Tarauni sun yi Allah-wadai da tallafin, inda suka yi amfani da shafukan sada zumunta wajen nuna fushinsu, a cewar rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka dura kan dan majalisar, sun nuna cewa su ba dawakai ba ne da za su ci dawa da gero a cikin watan Ramadana, kuma ace tallafi ne daga dan majalisar.
A cikin wani faifan bidiyo da wani Abba Wrecca, ya wallafa a shafinsa na Facebook, an nuna yadda jami’an tsaro suna dukan mutane a wajen karbar tallafin.
Rahoton ya nuna cewa jami'an tsaron na zane mutane ne domin tilasta su tsayawa a kan layi, duk da ranar da ake kwallawa, yayin da suke kokarin samun tallafin.
Abba Wrecca ya rubuta a shafinsa cewa:
“Ga dawa da geron da dan majalisa mai wakiltar Tarauni, wanda kuma surukin Rabiu Kwankwaso ne, yake rabawa."
Kalli bidiyon a kasa:
A wani bidiyo daban, wasu mazauna yankin sun bayyana takaicinsu kan yadda sauran ‘yan majalisa ke rabawa jama’arsu babura, filaye, da wasu kayan more rayuwa, yayin da a Tarauni ake rabon gero da dawa.
"Mu ba dawakai ba ne" - 'Yan mazabar Tarauni

Source: Facebook
Wani mazaunin yankin ya ce, “Na rantse da Allah, mahaifiyata ba za ta ci wannan abu ba a watan Ramadan.”
Wani mai sharhi, Umar Mai Rice, ya ce dalilin da yasa dan majalisar ya raba gero da dawa shi ne saboda ya tashi da cin su tun yana karami.
Dayyib Usman ya wallafa cewa:
“Mu ba dawakai ba ne. Ko ‘ya'ya doki ma sun daina cin dawa.”
Wani mai martani, Zakareeyah Xavi, ya ce:
“Ya kunyata mutanen mazabar Tarauni. A fada masa cewa shi wakilin jama’a ne, ba wakilin dawaki ba.”
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin mazauna yankin sun bar kayan tallafin a wurin rabon da aka gudanar a yankin Tarauni.
Sai dai magoya bayan dan majalisar sun mayar da martani, suna mai cewa ba dawa da gero kadai aka rabawa jama’a ba, an kuma raba shinkafa da wake.
Kalli dayan bidiyon a nan kasa:
Dan majalisa ya rabawa mutane 5000 tallafi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hon. Usman Zannah, ɗan majalisar Kaga/Magumeri/Gubio, ya tallafa wa al’ummarsa don rage wahala, musamman a lokacin azumin Ramadan.
Tallafin ya ƙunshi shinkafa, sukari, taliya da kudi, wanda aka ce ya saba rabawa domin jama’a su samu saukin gudanar da azumi a kowace shekara.
Hon. Zannah daga jihar Borno, ya jaddada kudirinsa na inganta ilimi, aikin gona, da samar da ayyukan yi domin kyautata rayuwar al’ummar mazabarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


