Ramadan: CAN Za Ta Yi Shari'a da Jihohin da Suka Rufe Makarantu, Ta Kafa Sharuda

Ramadan: CAN Za Ta Yi Shari'a da Jihohin da Suka Rufe Makarantu, Ta Kafa Sharuda

  • Kungiyar CAN ta bukaci jihohin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi su janye matakin rufe makarantu na makonni biyar don azumin Ramadan
  • Shugaban kungiyar CAN, Daniel Okoh, ya ce matakin na tauye hakkin dalibai da Musulmi ba kuma zai kara tabarbarewar ilimi a jihohin
  • CAN ta bukaci gwamnoni su yi tattaunawa da shugabannin addinai da iyaye don samar da mafita, tana mai cewa idan ba a janye ba, za ta dauki matakin shari’a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bai wa gwamnatocin jihohin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi wa’adin janye umarnin rufe makarantu na makonni biyar.

Kungiyar ta nuna damuwa kan matakin rufe makarantun har na tsawon makonni saboda azumin Ramadan.

Kungiyar CAN ta fusata bayan rufe makarantu saboda Ramadan
Kungiyar CAN ta yi barazanar shiga kotu da jihohin da suka rufe makarantunsu saboda Ramadan. Hoto: @presidentofCAN.
Asali: Twitter

Ramadan: CAN ta nuna damuwa kan rufe makarantu

Kara karanta wannan

Bauchi: Miji ya yi wa matarsa dukan tsiya har ta zarce lahira kan abincin Ramadan

A wata sanarwa da ƙungiyr ta wallafa a shafin Facebook, Shugaban CAN, Daniel Okoh, ya soki matakin yana mai cewa zai kara dagula matsalar ilimi a jihohin da ke da yawan yaran da ba sa makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daniel Okoh ya ce wannan mataki na nuna bambanci ne kuma take hakkin dalibai da ba Musulmi ba ne.

Kungiyar ta yi gargadi cewa idan ba a janye ba, za ta dauki matakin shari’a kan dukan jihohin.

CAN ta bukaci tattaunawa mai zurfi

Sanarwar ta ce:

“Ilimi hakki ne na kowa kuma ginshikin ci gaba, Rufe makarantu daga matakin firamare har zuwa jami’a na tsawon lokaci zai kawo cikas ga karatu kuma ya hana miliyoyin dalibai ci gaba.”
“Dole a yi tattaunawa mai zurfi tsakanin Musulmai, Kiristoci da sauran kabilu don tabbatar da adalci."
“Muna bukatar hadin kan ‘yan Najeriya don tabbatar da cewa addini da ci gaba suna tafiya tare, ba tare da cutar da ilimin ‘ya’yanmu ba."

Kara karanta wannan

Ramadan: Tinubu ya tura sako ga Musulmi, ya yi albashir kan farashin abinci da fetur

Okoh ya bayar da misali da kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ake daidaita jadawalin karatu maimakon rufe makarantu gaba daya.

Ya ce:

“A duniya, kasashe irin su Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ba sa rufe makarantu gaba daya saboda Ramadan, sai dai rage lokutan karatu."
CAN ta dauki zafi bayan rufe makarantu a Ramadan
Kungiyar CAN ta yi barazanar shiga kotu kan rufe makarantu a Ramadan. Hoto: Christian Association of Nigeria-CAN.
Asali: Facebook

CAN ta bukaci fifita ilimi a Arewa

Kungiyar CAN ta ce tana goyon bayan zaman lafiya tsakanin addinai, amma ba za ta yarda da matakin da zai hana ‘yan kasa hakkinsu na ilimi ba.

Kungiyar ta bukaci gwamnonin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi su tattauna da dukkan bangarori don samun mafita cikin lumana.

Idan ba a magance matsalar ba, CAN ta ce za ta dauki matakin shari’a don kare hakkin dalibai da ci gaban kasa.

A karshe, kungiyar ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su zauna lafiya, tare da tabbatar da cewa ba a tauye hakkin kowa ba.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna ya rufe dukkanin makarantun jiharsa na tsawon mako 5

Gwamnatin Bauchi ta rufe makarantu saboda Ramadan

Kun ji cewa Gwamnatin Bauchi ta sanar da rufe makarantu na gwamnati da na masu zaman kansu na tsawon makonni biyar gabanin Ramadan.

Sanarwar ta shafi makarantun firamare har zuwa na gaba da sakandare, yayin da aka ce hutun na cikin jadawalin karatun 2024-2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.