Gwamna Zai Kashe N634m kan Ƴaƴan Talakawa, Za a Biyawa Ɗalibai 23, 048 Kuɗin WAEC
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo, zai kashe N634m domin biyan kudin jarabawar WASSCE ga daliban makarantun gwamnati
- Sanarwar gwamnatin jihar Ondo ta bayyana cewa dalibai 23,048 da suka ci jarabawar karin girma ta JSS II ne za su ci gajiyar shirin
- Wannan mataki zai rage wa iyaye nauyin kudi tare da bai wa kowane dalibi damar zana jarabawar ba tare da wata matsala ta kudi ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo, ya amince da fitar da Naira miliyan 634 domin sanya farin ciki a fuskar 'ya'yan talakawa da ke karatu.
Gwamnan Onodo, ya amince a kashe kudin ne wajen biyan kudin jarabawar WASSCE ta shekarar 2024/2025, ga daliban makarantun sakandare na gwamnati a jihar.

Asali: Facebook
Gwamna zai biyawa dalibai 23,048 kudin WAEC
Mai magana da yawun gwamnan, Mista Ebenezer Adeniyan, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Akure a ranar Juma’a, inji rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce wannan mataki na daga cikin kokarin rage wa iyaye da masu kula da dalibai nauyin biyan kudin jarabawar.
Hakan zai bai wa dalibai 23,048 da suka ci jarabawar karin girma ta JSS II damar yin rajista domin zana jarabawar WASSCE na wannan shekarar.
Mista Ebenezer ya shaida cewa ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha ta jihar Ondo ce ke kula da zana jarabawar karin girman domin zakulo hazikan dalibai.
'Ya'yan talakawa za su yi ilimi mai zurfi
Sanarwar mai magana da gwamnan ta ce:
“A tsawon shekaru, gwamnatin jihar ta kasance tana daukar nauyin biyan kudin jarabawar WASSCE ga daliban makarantun gwamnati.
"Wannan matakin na gwamnati yana matukar saukakawa iyaye, ko masu rikon daliban, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.
“Jarabawar WASSCE tana da muhimmanci a fagen ilimi, domin ita ce ke ba dalibai damar samun ci gaba da karatu a manyan makarantun gaba da sakandare tare da samun dama a fannoni daban-daban na aiki.
“Gwamnati na ci gaba da daukar nauyin wannan jarabawa kowace shekara domin tabbatar da cewa kowane dalibi da ya cancanta na da damar yin jarabawar ba tare da wata matsala ta kudi ba.
“Wannan shiri zai rage bambance-bambance tsakanin dalibai daga gidajen masu hannu da shuni da na marasa karfi."
Gwamnan Ondo ya jaddada kudirin inganta ilimi

Asali: Twitter
Gwamnatin Ondo ta jaddada kudirinta na ci gaba da daukar nauyin biyan kudin jarabawar WASSCE, domin cimma kudurin gwamnatin Aiyedatiwa na inganta fannin ilimi.
Wannan mataki na gwamnatin Aiyedatiwa ya dace da manufofinta na bunkasa ilimi tare da tabbatar da cewa kowane yaro yana da damar samun ilimi mai zurfi.
Gwamnatin jihar ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da wannan shiri domin inganta makomar matasa da a cewarta su ne za su jagoranci jihar, kasar da ma duniya a nan gaba.
Gwamnan Kano zai tura dalibai 1002 karatu waje
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kano, karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bayyana shirin sake tura dalibai 1002 karatu a jami'o'in kasashen waje.
Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Gwarzo ya ce shirin zai bai wa matasan Kano damar samun ingantaccen ilimi, tare da gina basirar su a duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng