An Shiga Tashin Hankali da Wani Matashi Ya Kashe Amaryarsa Watanni 8 da Aurensu
- Wani matashi a jihar Edo, ya shiga hannun 'yan sanda bayan zargin kashe matarsa, Success Izekor, a gidansu da ke birnin Benin
- Rahoto ya nuna cewa Kelvin Izekor ya sanya adda, ya sassari Success a kai, lamarin da ya yi ajalinta, bayan shafe watanni suna rikici
- ’Yan sanda sun ce wasu matasa sun kusa kashe Kelvin da duka, amma aka kwace shi tare kai shi kotu, inda aka tura shi gidan yari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Wani mutum mai suna Kelvin Izekor, da ke zaune a Benin City, jihar Edo, ya shiga hannu da aka zarge shi da kashe matarsa, Success Izekor, mai shekara 38.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daren 22 ga watan Fabrairu, 2025, a gidansu da ke Upper Mission Extension, cikin birnin Benin City.

Asali: Twitter
Ana zargin ango ya kashe amaryarsa a Edo
Shaidu sun bayyana cewa Kelvin ya sanya adda ya sari matarsa a kai, ya ji mata mummunan rauni, wanda ya haddasa mutuwarta, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano cewa ma’auratan sun yi aure ne a watan Yunin 2024, kuma rahotanni sun nuna cewa makwabta sun sha ganin Kelvin na cin zarafin matarsa kafin ya kashe ta.
Kakakin rundunar ’yan sanda na jihar Edo, Moses Yamu, ya tabbatar da mutuwar Success a cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a ranar Alhamis.
Matasa sun kusa kashe mijin Success
Moses Yamu ya ce da misalin karfe 10:00 na dare, rundunar ta samu labari cewa wani mutum mai suna Kelvin Izekor da ke Upper Mission Extension ya kashe matarsa.
Jami'in dan sanda ya ce sun samu rahoto cewa wasu fusatattun matasa sun kusa kashe Kelvin da duka, saboda fusata da kisan da ya yiwa Success.
“Dakarun ’yan sanda daga ofishin Aduwawa sun hanzarta zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar da gawar matar cikin jini, dauke da raunuka sarar adda a kai."
- Moses Yamu.
Kotu ta iza keyar angon zuwa gidan yari

Asali: Twitter
Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa jami’an tsaro sun yi kokari sosai wajen kwantar da hankalin jama’a da kuma hana su daukar doka a hannunsu, kafin su kama wanda ake zargi.
“An dauki gawar mamaciyar zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarta,” a cewar Moses Yamu yayin da yake yin karin bayani a sanarwar.
Bayan kama Kelvin, sanarwar ta ce an gurfanar da shi a kotu, aka mika shi gidan yari yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.
Kwamishiniyar 'yan sanda ta gargadi ma'aurauta
Kwamishinan ’yan sandan jihar Edo, CP Betty Enekpen Isokpan Otimenyin, ta yi tir da yadda ake samun yawan rikici tsakanin ma’aurata da ke kai ga kisan kai.

Kara karanta wannan
Mutuwa mai yankar ƙauna: Allah ya yi wa mahaifi da kawun ɗan takarar gwamna rasuwa
Ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa za a gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Ta gargadi ma’aurata da su guji amfani da rikici wajen warware matsalolinsu, ta ce rundunar ’yan sanda za ta dauki matakin hana irin wannan mummunan al’amari ci gaba da faruwa.
Matashi ya kashe matarsa kan karamin abu
'A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sanda sun cafke wani magidanci a Akure, jihar Ondo, bisa zargin kashe matarsa bayan wata gardama da ta barke a tsakaninsu.
Binciken 'yan sanda ya gano cewa magidancin, Fatai Abdullahi, ya daba wa matarsa almakashi sakamakon rikicin da ke yawan kunno kai a tsakaninsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng