Miji ya kashe matarsa domin tana hana shi hakkin kwanciyar aure

Miji ya kashe matarsa domin tana hana shi hakkin kwanciyar aure

Wani magidanci mai suna John Onyeme da ke zaune a Ladi-Lak, Bariga a jihar Legas ya kashe matarsa, Esther Onyeme da duka saboda ba ta yarda tana ba shi hakkinsa na kwanciyar aure.

City Round ta ruwaito cewa matar, Esther Onyeme tana da mukami a coci kuma tana da makarantar frimare da sakandare a unguwar.

Makwabta sun ce John ya dade yana zargin cewa matarsa tana yawon zinace-zinace kuma ba ta bashi hakkinsa na kwanciyar aure wadda hakan ne sabibin yawan rikici tsakaninsu.

An gano cewa ma'auratan suna da yara biyu kuma suna zaune ne a Ayorinde Street, Ladi-Lak kafin watanni biyar da suka wuce matar da kwashe kayan ta ta koma coci da zama sakamakon fada da su kayi da mijin.

Rahotanni sun bayyana cewa Johan ya tafi cocin a ranar Juma'a 31 ga atan Janairun 2020 kuma ya lakada mata dukkan tsiya.

Miji ya kashe matarsa domin tana hana shi hakkin kwanciyar aure
Miji ya kashe matarsa domin tana hana shi hakkin kwanciyar aure
Asali: UGC

An ce an kwantar da ita a wani asibitin kudi amma ta mutu bayan kwanaki uku.

Wani mazaunin Ayorinde Street, Tope Adeyemo ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa matar ta sha kai karar mijinta caji ofis na 'yan sanda ke Pedro.

Adeyemo ya ce, "Ya dade yana dukar matan kuma tana kararsa a caji ofis na Pedro. Matar tana da makaranta. Mace ce mai kwazon aiki amma mijinta yana tsamanin tana bin maza tana zina da su ne."

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Bala Elkana ya ce an mika binciken zuwa sashin binciken manyan laifuka CIID da ke Yaba domin zurfafa bincike.

Ya ce wani Apostle Friday Ugorji ne ya zo ofishin 'yan sanda misalin karfe 9 na safen ranar 31 ga watan Yuli inda ya ce wani mutum mai suna John Onyeme ya yi wa matarsa Esther Onyeme dukkan tsiya har sai da ta mutu.

Faston ya ce shine ya kai ta asibiti domin ayi mata magana amma ta rasu bayan kwanaki uku. An ajiye gawarta a asibiti domin bincika sababin mutuwarta yayin da shi kuma wanda ake zargin yana hannun hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel