'Sun Sabawa Shari'a': Sultan Ya Bukaci Majalisa Ta Cire Wasu Sassa a Kudirin Haraji
- Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci (NSCIA) ta tura bukata ga Majalisar Dattawa kan sabon kudirin haraji da ke gabanta
- NSCIA ta bukaci majalisar ta cire sassan dokar haraji da suka saba wa Shari’a, musamman kan aure da gado da ke ciki
- Majalisar kolin ta mika bukatarta ga kwamitin kudi na Sanatoci tare da shawarar a maye wasu kalmomi don ka da a ware wasu addinai
- Shugaban kwamitin kudi na Majalisar Dattawa, Sani Musa, ya tabbatar da cewa duba dokokin haraji zai kasance a fili kuma bisa muradin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci (NSCIA) ta bukaci Majalisar Dattawa ta sake duba wasu wurare a kudirin haraji.
NSCIA ta bukaci cire sassan dokokin haraji da suka saba wa shari’a, musamman kan batun aure da gadon Musulmi.

Asali: Twitter
Bukatar Sultan ga Majalisa kan kudirin haraji
Hakan na kunshe a cikin wata takarda da ta gabatar ga kwamitin kudi na Majalisar Dattawa da Punch ta samu a yau Talata 25 ga watan Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma majalisar ta bukaci a sauya kalmar “ecclesiastical” da “religious” a wani sashe na dokar, domin guje wa ware wasu kungiyoyin addini.
Takardar ta bayyana cewa:
“NSCIA, a matsayinta na wakiliyar dukkan Musulmi a kasar nan, tana so a duba korafe-korafen da kungiyoyi daban-daban suka gabatar.”
“Dokar Najeriya ta 1999 (wanda aka yi wa gyara) ta tanadi kotun Shari’a don harkokin Musulmi kamar aure da gado, don haka duk sashe da ya saba ya kamata a cire shi.”
“Kalmar ‘ecclesiastical’ da aka yi amfani da ita a dokar haraji ya dace a sauya ta da ‘religious’ domin kada a rage wa wasu addinai daraja.”

Tabbacin da majalisa ta bayar kan kudirin haraji

Kara karanta wannan
Sanatan da ya koma APC na fuskantar barazana daga ƴan mazabarsa, sun kai shi kotu
NSCIA ta bukaci Majalisar Dattawa ta amince da dokar haraji bayan an duba shawarwarin da ta bayar, tana mai godewa damar da aka bata don ta yi bayani.
NSCIA, karkashin jagorancin Shugabanta, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar II, ita ce babbar kungiya da ke kula da harkokin Musulunci a Najeriya.
Majalisar Dattawa kwanan nan ta shirya taron jin ra’ayin jama’a kan dokokin haraji, inda kwararru daga bangarorin tattalin arziki da kudi suka halarta.
Shugaban kwamitin kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Sani Musa, ya tabbatar da cewa shirin zai kasance a fili kuma bisa muradin kasa, cewar Tribune.
Ya jaddada cewa taron ya na da nufin duba dokokin haraji da yin gyara domin su dace da halin tattalin arziki na yanzu.
Sultan ya shawarci malamai da sauran Musulmi
A baya, kun ji cewa yayin da ake shirin fara azumin watan Ramadan, Kungiyar jama'atu Nasrul Islam (JNI) ta buƙaci malamai su haɗa kansu a wannan lokaci.
Kungiyar da ke karkashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce bai kamata sabanin fahimta ya rika jawo faɗa tsakanin musulmai ba.
Sultan ya ja kunnen malamai su daina zagin juna musamman a wurin karatuttukansu yayin za a fara azumin Ramadan nan sa yan kwanaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng