Soyayya Ta Ƙare: Wani Ɗan Najeriya Ya Lakaɗawa Budurwarsa Dukan Tsiya har Ta Mutu

Soyayya Ta Ƙare: Wani Ɗan Najeriya Ya Lakaɗawa Budurwarsa Dukan Tsiya har Ta Mutu

  • Rundunar ‘yan sandan Legas ta kama wani matashi, Gbolahan Adebayo, bisa zargin lakadawa budurwarsa duka har ta mutu
  • Wani mazaunin yankin ya ce an ji ihun marigayiyar tana neman agaji da tsakar dare lokacin Gbolahan na dukanta kafin mutuwarta
  • Kakakin ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da mutuwar budurwar tare da bayyana matakin da aka dauka kan matashin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani matashi mai shekaru 23, Gbolahan Adebayo, bisa zargin lakadawa budurwarsa duka har ta mutu.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin Ijedodo da ke cikin karamar hukumar Alimosho, a jihar Legas.

Rundunar 'yan sanda ta cafke matashin da ya kashe budurwarsa da duka a Legas
Legas: Wani matashi ya shiga hannu bayan kashe budurwarsa da duka. Hoto: @LagosPoliceNG
Asali: Twitter

Rahotan jaridar Punch ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a yayin da marigayiyar ta ziyarci gidan saurayin nata.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda saurayi ya kashe budurwarsa da duka

Wani mazaunin yankin mai suna Akin ya shaida wa manema labarai cewa an ji ihun marigayiyar tana neman agaji a tsakar dare lokacin da saurayin nata ke dukan ta.

Akin ya ce an dauki kusan awa daya ana ci gaba da jin ihunta, sai kuma daga bisani aka daina jiyuryar o mbudurwar.

Washe garin ranar, Adebayo ya fara neman taimako, inda mazauna yankin suka shiga dakinsa suka tarar da budurwarsa kwance ba ta motsi, inji Akin.

‘Yan Sanda sun tabbatar da faruwar lamarin

Kakakin rundunar 'yan sandan Legas ya tabbatar da mutuwar budurwar
Legas: CSP Benjamin Hundeyin ya ce an cafke matashin da ya kashe budurwarsa da duka. Hoto: @BenHundeyin
Asali: Twitter

Wani jami’in dan sanda da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa wani makwabcin Adebayo ne ya kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Isheri-Oshun a ranar Lahadi.

Jami’in ya ce an yi kokarin ceton budurwar bayan an kai ta asibiti, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an ga alamun duka a jikin marigayiyar.

Kara karanta wannan

Akpabio da shugabanni da jami’ai 3 da aka taba tuhuma da cin zarafin mata

Ya ce an dauki gawarta zuwa dakin ajiye gawa na IDH da ke Yaba domin gudanar da bincike.

Matakin da aka dauka zuwa yanzu

CP Benjamin Hundeyin ya shaida cewa:

“An samu rahoto daga wani makwabcin wanda ya ji Gbolahan Adebayo yana dukan budurwarsa da misalin karfe 2:00 na dare.
"Amma zuwa karfe 7:00 na safe, sai Adebayo ya fara ihun neman agaji, inda makwabta suka tarar da budurwar tasa kwance ba motsi.”
"Binciken farko ya nuna cewa akwai alamun duka a jikinta, kuma an dauki hotunan gawarta domin ci gaba da bincike."

Rahoton ya nuna cewa 'yan ssanda sun kama Adebayo nan take, kuma yanzu haka ana ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru kan lamarin.

Saurayi ya kashe budurwarsa bayan gama badala

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani matashi, Muhammad Ibrahim, ya kashe budurwarsa bayan ta nemi ya biya ta N5,000 bayan sun kammala aikata lalata.

Rigima ta barke tsakaninsu kan biyan kudin, inda ta rikide zuwa fada mai zafi. A karshe, Ibrahim ya daba wa budurwar wuka, wanda hakan ya kai ga mutuwarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.