Bayelsa: Matashi ya Lakadawa Budurwarsa Dukan 'Kawo Wuka', Tace ga Garinku

Bayelsa: Matashi ya Lakadawa Budurwarsa Dukan 'Kawo Wuka', Tace ga Garinku

  • Wani matashi mai shekaru 30 da doriya ya halaka budurwarsa mai shekaru 22 bayan wata yar hatsaniya ta rincabe tsakanin masoyan biyu a jihar Delta
  • An gano yadda Arepamowei Koru da Toma Serve-God Angolo ke zaman kansu cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna kafin matashin ya lakada wa matar bakin duka
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar yayin tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana yadda aka cafke wanda ake zargin

Bayelsa - Wani matashi mai shekaru 30 da doriya mai suna Arepamowei Koru a anguwar Ogobiri cikin karamar hukumar Sagbama da ke jihar Bayelsa, ya lakadawa budurwarsa mai shekaru 22, mai suna Toma Serve-God Angolo duka har lahira.

Taswirar Bayelsa
Bayelsa: Matashi ya Lakadawa Budurwarsa Dukan 'Kawo Wuka', Tace ga Garinku. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

An gano yadda masoyan biyu ke zaman kansu a anguwa da matashin yake kafin aukuwar lamarin ranar Talata, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana tsadar abinci, dakin ajiyan kamfanin abinci ya kone kurmus

Mazauna yankin sun shaidawa City & Crime yadda masoyan biyu ke rayuwa tare ba tare wata hatsaniya ba kafin daga bisani wani 'dan rashin jituwa ya hada su ranar wanda ya kai ga wannan kaddararren fadan.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, kakakin 'yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana yadda aka cafke wanda ake zargin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba wannan bane karon farko da ake jin saurayi yana halaka budurwarsa duk kuwa da tsananin soyayyar da ke tsakaninsu.

Sau da yawa karamar hayaniya kan hada masoya, inda hakan za a ga ya zarce kuma ya tarar da ajali wanda kan sa a rasa rai.

Mata kansu da yawa suna halaka mazansu ko kuma masoya, duk kuwa da irin kauna, jin kai da tausayin da aka san su da shi.

Ana tsaka da bikin aure, wani ya tada hankalin ango

Kara karanta wannan

Allah yayi wa Fitaccen Furodusa Kuma Jarumi Abdulwahab Awarwasa Rasuwa

A wani labari na daban, wani ango ya fada tashin hankali wanda ya kasa boyuwa a idonsa yayin da ake tsaka da shaglin aurensa da masoyiyarsa.

Wani matashi ya mikawa amaryar da ke cikin kwalliya wasika wacce hakan yasa hankali da tunanin ango ya koma kan ta.

Amaryar ta bude wasikar inda ta ga ba wani abu bane face fatan alheri da aka taya su tare da musu fatan zaman lafiya a sabuwar rayuwar da za su fara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel