Gwamati Ta Tabbatar da Barkewar Zazzabin Lassa a Jihar Arewa, Mutum 3 Sun Mutu
- Gwamnatin jihar Benue ta sanar da barkewar cutar zazzabin Lassa bayan da aka samu karuwar yawan masu kamuwa da cutar
- Kwamishinan lafiya, Yanmar Ortese, ya ce mutane 40 aka yi wa gwaji, aka tabbatar da mutum 5 sun kamu, sannan uku sun mutu
- Wannan na zuwa ne yayin da hukumar NCDC ta sanar da cewa mutane 80 sun mutu a Najeriya a cikin 2025 bayan kamuwa da Lassa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue – Gwamnatin jihar Benue ta sanar da barkewar cutar zazzabin Lassa bayan karuwar yawan masu kamuwa da cutar a cikin shekaru hudu da suka gabata.
Kwamishinan lafiya da kula da jin dadin jama’a na jihar, Dakta Yanmar Ortese, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Makurdi.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi

Asali: UGC
Zazzabin Lassa: Mutane 3 sun mutu a Benue
Dakta Yanmar ya shaida cewa mutane 40 aka yi wa gwajin cutar, inda aka tabbatar da mutum 5 sun kamu, yayin da uku suka mutu, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan lafiya da kula da jin dadin jama'a na Benuwai ya nuna cewa mutuwar mutane uku ya nuna kashi 60% na yawan mace-mace daga cutar a bana.
Haka kuma, kwamishinan ya nuna damuwa kan yawaitar cizon maciji da ake samu jihar, yana mai cewa an samu rahoton mutane 199 da maciji ya ciza.
Dakta Yanmar ya ce a samu rahotanni ne daga babban asibitin Gbajimgba, da ke karamar hukumar Guma tsakanin Yuli zuwa Disambar 2024 kadai.
Alamomi da matakan dakile cutar zazzabin Lassa
Ya ce zazzabin Lassa wata cuta ce mai tsanani da ke yaduwa ta hanyar cudanya da beraye da suka kamu da ita ko kuma fitsarinsu da bayan gida.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30
Alamomin cutar sun hada da zazzaɓi mai zafi, ciwon kai, ciwon makogwaro, ciwon tsoka, ciwon kirji, amai, zawo, da yuwuwar zubar jini daga gabobi idan ta tsananta.
A kokarin dakile yaduwar cutar, gwamnatin jihar ta kaddamar da shirye-shirye na kawar da beraye ta hanyar tsaftace muhalli da wayar da kan jama’a kan yadda za su kare kansu daga cutar.
Kwamishinan ya shawarci jama’a da su rika ajiye abinci a rufaffen wuri, su kiyaye tsafta a gidajensu, kuma su gaggauta kai rahoton duk wanda ake zargi da cutar.
Lassa: NCDC ta tabbatar da mutuwar mutum 80

Asali: Twitter
A watan Fabrairu, hukumar NCDC ta bayyana cewa adadin wadanda suka kamu da cutar ya ragu daga mutum 68 a mako na biyar na shekarar 2025 zuwa mutum 54.
Wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a wannan lokaci sun fito daga jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Edo, Benue, Gombe, da Kogi.
A mako na shida na 2025 kadai, an samu jimillar mace-mace 80, wanda ke da kaso 19.4% na yawan wadanda suka mutu daga cutar – wanda ya fi yawan kashi 17.5% da aka samu a daidai wannan lokaci a shekarar 2024.
A jimlace, jihohi 11 ne suka tabbatar da bullar cutar a akalla kananan hukumomi 63, kamar yadda rahoton NCDC da Legit Hausa ta gani ya nuna.
Rahoton ya nuna cewa:
"Kashi 73% na dukkan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar sun fito daga jihohin Ondo, Edo, da Bauchi, yayin da sauran kashi 27% suka fito daga wasu jihohi takwas.
"Cikin wadannan jihohi, Ondo ce ke da mafi yawan adadin masu cutar da kashi 34%, sai Edo da kashi 21%, sannan Bauchi da kashi 18%.
"Mutanen da suka fi kamuwa da cutar su ne masu shekaru 21 zuwa 30, inda matsakaicin shekarunsu ke kaiwa 32."
Cutar zazzabin Lassa ta barke a jihar Bauchi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bauchi ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Lassa a kananan hukumomi bakwai na jihar.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa cutar ta bulla a kananan hukumomin da suka hada da: Bauchi, Toro, Kirfi, Tafawa Balewa, Dass, Ganjuwa, da Alkaleri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng