Ana Zargin Yana Tsakiyar Fada da El Rufai, Uba Sani Ya Samu Mukami a Gwamnatin Tinubu

Ana Zargin Yana Tsakiyar Fada da El Rufai, Uba Sani Ya Samu Mukami a Gwamnatin Tinubu

  • Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin PreCEFI don tabbatar da aiwatar da shirin Aso Accord, da aka samar don gyara tattalin arziki
  • Kwamitin zai yi aiki ne ta hannun GovCo da TechCo, domin tabbatar da cewa an cimma manufofin tattalin arzikin shugaba Bola Tinubu
  • Daga cikin mambobin kwamitin akwai, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin shugaban kasa kan hada-hadar tattalin arziki da kudin jama’a (PreCEFI) don sa ido kan aiwatar da shirin Aso Accord.

Manufar Aso Accord ita ce hanzarta aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki na gwamnati, tare da mai da hankali kan ci gaba da rage gibin kudi a cikin kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta kaddamar da kwamishinonin haraji guda 50

Kashim Shettima ya yi magana da ya kaddamar da kwamitin gyaran tattalin arziki na PreCEFI
Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da kwamitin gyaran tattalin arziki na PreCEFI. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

Gwamnati ta kaddamar da kwamitin PreCEFI

Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya kaddamar da kwamitin a ranar 10 ga Fabrairu, 2025, don tabbatar da kudirin gwamnati, kamar yadda ya sanar a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya ce wannan wani mataki ne na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cimma burin tattalin arzikin Najeriya ya kai dala tiriliyan daya ta hanyar manufofi masu karfi.

Ya ce kwamitin zai yi aiki ne ta hannun kwamitoci biyu, wato kwamitin gudanarwa (GovCo) da kwamitin fasaha (TechCo), tare da goyon baya daga ofishin aiwatarwar da shirin.

Bayani kan ayyukan kwamitin GovCo

A cewar bayanan da aka fitar a ranar Talata, mataimakin shugaban kasa ne ke jagorantar kwamitin gudanarwa (GovCo), yayin da ministan kudi, Wale Edun ke matsayin Mataimaki.

"Kwamitin GovCo zai yi jagoranci da sa ido kan ayyukan EFI, ya tabbatar da daidaito da tsare-tsaren ci gaban kasa da samar da kudade," inji sanarwar Shettima.

Kara karanta wannan

"Raba daidai ake yi," Gwamnatin Tinubu ta ce babu son rai a salon mulkinta

Daga cikin muhimman aikace-aikacen kwamitin akwai yin jagoranci da sa ido kan aiwatar da shirin Aso Accord tare da tabbatar da ingantaccen tsarin shugabanci.

Haka nan, kwamitin zai cimma alkawurran aiki, sa ido da tantance ci gaban manyan ayyukan da ake aiwatarwa don tabbatar da kammalawarsu.

Bugu da kari, kwamitin zai zama tsani tsakanin majalisar tattalin arzikin kasa da hukumomin da ke aiwatar da shirin hada-hadar tattalin arziki da kudi.

'Yan kwamitin GovCo da aka nada

Shettima ya kaddamar da 'yan kwamitin PreCEFI na gyaran tattalin arzikin Najeriya
Uba Sani, Nuhu Ribadu da jerin 'yan kwamitin PreCEFI na gyaran tattalin arziki. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

Mambobin kwamitin sun hada da mataimakin shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Sanata Ibrahim Hadejia, da gwamnan jihar Enugu, Dakta Peter Ndubuisi Mbah.

Sauran mambobin sun hada da gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani da ministan sadarwa, kirkire-kirkire, da tattalin arzikin zamani, Dr. Bosun Tijani.

Ministan harkokin jin kai da yakar talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe, da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, na cikin kwamitin.

Kara karanta wannan

Rumbun sauki: Gwamna ya bude wuraren sayar da abinci da araha ga talakawa

Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, da shugaban IQS Africa, Farfesa Emmanuel Itapson, na wakiltar manyan bangarorin kudi da masu kamfanoni.

Sakataren kwamitin shi ne Dr. Nazifi Abdullahi Zurmi, wanda ke matsayin mashawarcin shugaban kasa kan hada-hadar tattalin arziki da kudin jama’a.

Bayani kan ayyukan kwamitin TechCo

Sanarwar ta ce an dorawa kwamitin fasaha (TechCo) alhakin aiwatar da tsare-tsaren da GovCo ya tsara, tare da tabbatar da dacewar su da ingancin aiwatarwa.

Mataimakin shugaban kasar ya ce:

"An dorawa kwamitin TechCo alhakin bayar da jagoranci na fasaha da tabbatar da cewa an aiwatar da shirin EFI yadda ya kamata.
"Wani bangare na aikinsa shi ne nazarin dabarun GovCo domin aiwatarwa, zai tabbatar da cewa kowane shiri na iya kammaluwa cikin sauki.
"Kwamitin fasahar zai tsara hanyoyin aiwatar da shirye-shiryen EFI, sa ido kan kasafin kudi, da tabbatar da dacewar tsare-tsaren da Aso Accord ya kawo.

Kara karanta wannan

Yadda Sanatoci suka jawo hankalin Tinubu ya waiwayi gyaran titunan Arewa

"Haka nan, kwamitin yana da alhakin tsara sababbin hanyoyin warware matsalolin hada-hadar tattalin arziki da kudin jama’a a Najeriya."

2027: Uba Sani ya kalubalanci El-Rufai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Uba Sani, ya ƙalubalanci tsohon gwamna, Nasir El-Rufai da ƴan siyasar da ke shirin haɗa kai domin kawar da Bola Tinubu a 2027.

Uba Sani ya ce duk wanda ke da burin kalubalantar shugaban ƙasar a zaɓe mai zuwa, ya fito ya gwada farin jininsa, maimakon ya labe yana shiri ta bayan fage.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.