Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Sakataren Karamar Hukuma da Mutum 4 a Arewa

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Sakataren Karamar Hukuma da Mutum 4 a Arewa

  • 'Yan bindiga sun farmaki gidan sakataren karamar hukumar Munya a Neja da tsakar dare, sun sace shi tare da wasu mutane huɗu
  • Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa 'yan bindigar sun kutsa gidan sakataren da misalin ƙarfe 10:00 na daremn ranar 20 ga Fabrairu
  • An ce 'yan bindigar sun tsere da wanda suka sace zuwa yankin Chikun, da ke Kaduna, yankin da suke amfani da shi wajen fakewa
  • Jami’an tsaro sun bazama dazuka domin ceto mutanen da aka sace, amma har yanzu babu tabbacin an ceto su ko ana ci gaba da nema

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - An shiga tashin hankali a jihar Neja yayin da wasu 'yan bindiga suka kai farmaki gidan wani sakataren karamar hukuma da tsakiyar dare.

'Yan bindigar dauke da mugayen makamai sun sace sakataren karamar hukumar Munya, Alhaji Daina Usman da wasu mutane hudu.

Kara karanta wannan

Ginin makaranta ya rufta kan ɗalibai suna tsakiyar karatu a Yobe, an rasa rai

Majiyoyi sun bayyana yadda 'yan bindiga suka sace sakataren karamar hukuma a Neja
'Yan bindiga sun sace sakataren karamar hukumar Munya da ke jihar Neja. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Neja: 'Yan bindiga sun sace sakataren Munya

Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa majiyoyin tsaro sun tabbatar da wannan farmakin da 'yan bindigar suka kai yankin Sarkin Pawa da ke jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun shaida cewa 'yan ta'addar sun farmaki gidan sakataren karamar hukumar da misalin karfe 10:00 na daren ranar 20 ga watan Fabrairu.

"Yan bindigar, cikin kwarewa, sun farmaki gidan sakataren karamar hukumar da ke kusa da gabar tekun Sarkin Pawa, wani yanki da ke fuskantar hare-hare."

- Inji rahoton.

'Yan bindigar sun nausa zuwa jihar Kaduna

Daga cikin wadanda 'yan bindigar suka tafi da su akwai: Daina Usman (sakataren karamar hukumar), matarsa, Debora Daina, Sati Daina, Gambo Shagari da Sorro (Snu).

Majiyoyin sun shaida cewa 'yan bindigar sun hazarta tserewa da wadanda suka yi garkuwa da shi zuwa karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

An ce karamar hukumar Chikun ta kasance wani labi da 'yan bindigar da ke amfani da ita wajen tserewa da wadanda suka sace a yankin.

Kara karanta wannan

Adamawa: An shiga fargaba da bindiga ta tashi a wurin ibada, mutane sun jikkata

Jami'an tsaro sun fita farautar 'yan bindigar

Rahoton ya nuna cewa jami'an tsaron hadin gwiwa da suka kunshi: Sojoji daga Forward Operating Base (FOB), Sarkin Pawa, 'yan sandan Neja da 'yan banga sun bi bayan 'yan bindigar.

An ce jami'an tsaron hadin gwiwar sun fantsama dazuzzukan yankin domin gano 'yan bindigar da kuma tabbatar da kwato wadanda aka sace.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton, babu tabbacin ko an kwato wadanda aka sacen, ko kuma ana ci gaba da farautarsu.

'Yan bindiga sun sace shugaban karamar hukuma

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a jihar Benue, inda suka yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Ukum, Haanongon Gideon.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace Gideon ne tare da wasu mutum uku yayin da yake kan hanyarsa zuwa jana’izar Sarkin ƙaramar hukumar Katsina-Ala.

Lamarin ya haifar da fargaba a yankin Ukum, inda jama’a ke kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakin ceto waɗanda aka sace a cikin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.