Yanzu-Yanzu: An Sace Sakataren Jam'iyyar APC a jihar Rivers

Yanzu-Yanzu: An Sace Sakataren Jam'iyyar APC a jihar Rivers

  • Ƴan bindiga sun kai farmaki jihar Rivers inda suka yi awon gaba da wani babban jigo kuma shugaba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Ƴan bindigan dai sun je har gida sannan suka tafi da sakataren jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar
  • Wani babban jigo a jam'iyyar APC ta jihar ya tabbatar da sace sakataren da ƴan bindigan suka yi

Jihar Rivers- Ƴan bindiga sun sace wani babban jigo kuma sakataren jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Mr Amadi Osaronu a ƙaramar hukumar Ikwerre ta jihar Rivers.

Ƴan bindigan sanye da kayan ƴan sanda sun je har gida sannan suka sace Osaronu a gidansa dake a Aluu, cikin ƙaramar hukumar Ikwerre, a ranar Laraba. Rahoton The Punch

Bindiga
Yanzu-Yanzu: An Sace Sakataren Jam'iyyar APC a jihar Rivers Hoto: Punch
Asali: UGC

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC a jihar, Darlington Nwauju, shine ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zabe, Burin Jam'iyyar Peter Obi Na Samun Gwamna Ya Samu Tawaya, Dubunnan Mambobin Jam'iyyar Sun Koma PDP

“Duk irin tsangwama da sanya tsoro a zukatan mutane da wata irin kitimurmura bata isa ta sauya shan kashin da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zata yi ba." A cewar sa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙarin bayani na nan tafe.....

Ana Daf Da Zabe, Makisa Sun Kai Wa Dan Takarar Gwamnan PDP Hari

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar gwamnan jihar Delta a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya sha da ƙyar a hannun ƴan bindiga.

Ƴan bindigan dai sun kai farmaki ga tawagar motocin ɗan takarar gwamnan, Hon Sheriff Oborevwori wanda shine shugaban majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng