Kano Ta Cika Ta Batse: An Daura Auren Amina, 'Yar Sarki Sanusi da Angonta Ma'aji

Kano Ta Cika Ta Batse: An Daura Auren Amina, 'Yar Sarki Sanusi da Angonta Ma'aji

  • Gimbiya Amina, ‘yar Sarkin Kano, ta angwance da Muhammad Ma’aji a bikin aure mai kayatarwa da aka yi a ranar 14 ga Fabrairu
  • Amarya ta yi kyau cikin kaya na alfarma, yayin da bikin ya samu halartar jama’a, ciki har da sarakuna, 'yan siyasa da manyan attajirai
  • Manyan mutane, ciki har da Gwamnan Kano Abba Yusuf, Rabiu Musa Kwankwaso sun halarci bikin, wanda aka yi shi cike da tsari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Jihar Kano ta yi cikar fari a ranar 14 ga Fabrairu, 2025, yayin da aka daura auren Gimbiya Amina, ‘yar Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, da Muhammad Ma’aji.

An daura auren a Kofar Kudu da ke fadar Sarkin Kano a cikin wani yanayi mai kayatarwa da ya samu halartar manyan baki a ciki da wajen Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook

An daura auren Gimbiya Amina, diyar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
Gwamna Abba, Kwankwaso sun halarci daurin auren 'yar gidan sarkin Kano, Sanusi II. Hoto: @masarautarkano (X)
Asali: Twitter

An daura auren 'yar sarkin Kano, Sanusi

Amarya ta yi kyau a cikin riga fara da dogon mayafi, yayin da mijinta ya saka kaya na gargajiya iri ɗaya da na iyayenta, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangi da abokai sun shaida yadda amarya da ango suka yi tattaki tare, cikin farin ciki, bayan an kammala daurin aure.

Bikin gargajiya da aka yi, ya fito kimar gidan sarauta, inda aka sake ganin amarya a cikin wasu kaya masu launin jikin dawisu.

Ango da Amarya sun burge mutane

Daya daga cikin lokutan da suka fi jan hankali shi ne lokacin da diyar Sarki Sanusi II ta shiga cikin dakin taron bikin tare da ‘yan uwanta mata biyu.

An rahoto cewa ango ya nuna kauna ga amaryarsa a fili ta hanyar satar kallonta a kai a kai, abin da ya kara burge jama'a.

An ce biki ya yi biki, yayin da kawayen amarya suka yi ado da kaya masu launin ruwan dorawa, lamarin da kara wa taron armashi.

Kara karanta wannan

An yi kare jini biri jini tsakanin Boko Haram da ISWAP, da dama sun mutu

Abba, Kwankwaso, sun halarci daurin aure

Baki daga sassa daban-daban sun halarta, inda aka yi 'yan raye-raye da murna don taya sababbin ma'auratan murna.

Gwamnan Kano, Abba Yusuf, da matarsa Maryam, da Kakakin Majalisar Kano, Jibril Falgore, na daga cikin manyan baki da suka halarta.

Hakazalika, a hotunan da shafin Masarautar Kano na X ya wallafa, inda aka ga Gwamna Abba, Sanata Rabiu Kwankwaso a cikin wadanda suka halarci daurin auren.

Kalli hotunan a nan kasa:

Diyar Sarki Sanusi ta yi saukar AlKur'ani

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Maryam Sanusi (Inna), ‘yar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, mai shekaru tara, ta yi saukar karatun Al-Kur’ani.

Maryam ita ce ‘yar autar sarki kuma diya ga matar sarki ta biyu, wanda hakan ya kara farin ciki ga iyalinta, ta kai har sarkin ya halarci taron da kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.