Ku kalli kayatattun hotunan diyar Sarki Sanusi lokacin bikin saukar alqur'anin ta (Hotuna)
- Yar Sarkin Kano Mai Shekaru Tara Ta Sauke Kur'ani
- Maryam Sanusi (Inna) Mai Shekaru Tara Da Haihuwa 'Yar Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll, Ta Yi Saukar Karatun Al-kur'ani, Inda Aka Yi Bikin Saukar A Ranar Asabar

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai 7 ga watan nan na Janairu 'yar'autar sarkin Kano Muhammadu Sanusi II mai sina Maryam Sanusi yai bikin saukar alqur'ani a fadar sarkin na Kano kuma mahaifinta.

Ita dai Maryam ance itace yar'autar sarkin kuma diyace ga matar sarkin ta biyu. Mahaifin yarinyar da ya samu halartar bikin inda kuma ya mikawa diyar tasa takardar shaidar kammala saukar tata. A tare da shi sarkin hadda sauran yan uwan yarin yar da kuma abokan arziki.
Muna taya ta murna!
Asali: Legit.ng