Hoton diyar Sarki Sanusi tana 'hannu' da Osinbajo ya janyo muhawara mai zafi

Hoton diyar Sarki Sanusi tana 'hannu' da Osinbajo ya janyo muhawara mai zafi

Hoton Gimbiya Khadija Lamido Sanusi, daya daga cikin 'ya'yan Sarkin Kano, Sanusi Lamido II, tana tana gaisawa tare da yin hannu da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yayin da mahaifinta ke gabatar da ita ga mataimakin shugaban kasar yayin wani taro a Abuja da aka gudanar a karshen mako ya janyo muhawarra mai zafi a "Arewa Twitter", wani sashi na Twitter inda 'yan arewacin Najeriya suka bayyana ra'ayoyinsa kan harkokin yau da kullum.

A bangare guda akwai wadanda ke ganin cewa yin gaisawa da ta yi da mataimakin shugaban kasar haram ne saboda wasu kuma na ganin cewa babu laifi cikin tattare da abinda da aikata kamar yadda LIB ta ruwaito.

Wani muhawwara mai kama da wannan ya taba tasowa a kwanakin baya yayin da Ministan Sadarwa, Aliyu Pantami ya hana Shugaba Muhammadu Buhari yin hannu da wasu mata yayin wani taro kamar yadda wasu kafafen yadda labarai suka ruwaito.

Hoton diyar Sarki Sanusi II tana hannu da Osinbajo ya janyo cece-kuce
Hoton diyar Sarki Sanusi II tana hannu da Osinbajo ya janyo cece-kuce
Asali: Twitter

Ga dai ra'ayoyin wasu daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.

DUBA WANNAN: Ba bu matsin lambar da zai sa in saki El-Zakzaky - El-Rufai

@SaddiqB25 ya ce: Haram! Haram! Haram! Haram! Haram! Haram! Haram! Haram! ...

@Juliobam22 ya ce: Yayin da talakawan da ke munafintan kansu za su rika ihun cewa haramun ne ta gaida da na miji (mataimakin shugaban kasa). Allah ya yi maganin talauci (Na ajihu da na zuci)

@Timerexxl ta ce: Na ji dadin abinda ka fada daga karshe (talaucin zuci da na aljihu) saboda wasu na da kudi amma babu hikima

@aliyukankarofi ya ce: Kamata ya yi wannan mutumin ya rika bayar da misali na koyarwar musulunci amma turawan yamma ya ke wakilta. @masarautarkano don Allah ku fada masa cewa haramun ne ya rika karfafawa diyars gwiwa tana gaisawa da mazan da ba muharramanta bane.

@aaaisha33 ta ce: Maganar gaskiya idan za mu yi koyi da sunnan Annabi Muhammad (SAW). Babu inda ya gaida da macen da ba muharramansa bane. Idan kuma akwai, ka kawo hadisin don kare hujjar ka. Ina jira.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel