Tinubu Ya ba da Umarni a Dauki Ma'aikatan Lafiya 150 Aiki, An Ji Inda Za a Tura Su

Tinubu Ya ba da Umarni a Dauki Ma'aikatan Lafiya 150 Aiki, An Ji Inda Za a Tura Su

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince a dauki likitoci 50 da malaman jinya 100 aiki don inganta kiwon lafiya a gidajen gyaran hali
  • Gwamnatin tarayya ta ce za a tura likitocin hukumar NYSC zuwa gidajen kaso domin kula da lafiyar fursunoni da kare hakkinsu
  • An kammala gyaran gidan yarin Kuje, wanda yanzu ke da sabon asibiti, dakunan kwana na zamani, da ingantaccen ruwan sha

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da daukar likitoci 50 da malaman jinya 100 aiki don inganta kula da lafiya a gidajen yari.

Wannan yunkuri na daga cikin dabarun da gwamnatin Tinubu ke bi don magance matsalolin kiwon lafiya a gidajen yarin Najeriya.

Ministan harkokin cikin gida ya yi magana da Tinubu ya amince a dauki ma'aikatan lafiya 150 aiki
Tinubu ya amince a dauki ma'aikatan lafiya 150 aiki, za a tura su gidajen yari. Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya amince a dauki ma'aikatan lafiya

Babban mataimaki na musamman ga ministan harkokin gida, Babatunde Alao, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ta nemi ba ni rashawar N5bn," Ɗan takarar shugaban ƙasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce ministan harkokin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da amincewar shugaba Tinubu kan daukar ma’aikatan kiwon lafiyar.

Ya kara da cewa za a tura likitoci da yanzu ke yi wa kasa hidima (NYSC) zuwa gidajen yari don kula da lafiyar fursunoni.

Gwamnatin ta kara wa'adin ritayar likitoci

Ministan ya ce an amince da tsawaita wa’adin aiki ga ma’aikatan lafiya masu gab da ritaya don cike gibin rashin ma’aikata.

Wannan shirin na daukar ma’aikata zai taimaka wajen rage rashin aiki da kuma inganta kiwon lafiya, musamman a jihohi kamar Rivers.

Tunji-Ojo ya ce:

“Gwamnati ta jajirce ainun wajen inganta walwalar fursunoni da tabbatar da cewa an kula da lafiyarsu yadda ya kamata.”

Gwamnatin tarayya ta gyara gidan yarin Kuje

Sanarwar ta ce an kuma kammala gyare-gyare a gidan yarin Kuje, ciki har da gina sababbin dakunan kwana, ingantaccen ruwan sha, da sabon asibiti.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya yi dabarar sanya Tinubu kashe Naira biliyan 33 a aikin titi

Sabbin matakan da aka dauka suna da nufin inganta rayuwar fursunoni tare da samar da aikin yi ga matasan da suka kammala makaranta.

A cewar ministan, wannan matakin zai kara karfin tsarin kula da lafiya a gidajen yari, tare da tabbatar da cewa an bi ka’idar kare hakkin dan Adam.

Likitoci 59 sun ajiye aiki a Nasarawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kimanin likitoci 59 sun ajiye aiki a asibitin kwararru na Dalhatu Araf (DASH), Lafiya, jihar Nasarawa, saboda rashin isasshen albashi.

Ajiye aikin ya biyo bayan yajin aiki da zanga-zangar da likitocin suka yi, inda suka nemi gwamnati ta biya bukatunsu, amma ba su samu nasara ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.