'Dan Majalisa Ya Fadi Dalilin Kara N700bn a Kasafin Kudin 2025

'Dan Majalisa Ya Fadi Dalilin Kara N700bn a Kasafin Kudin 2025

  • Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2025 da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar
  • Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar ya bayyana dalilin yin ƙarin N700bn a kasafin kuɗin shekarar bana
  • Hon. Abubakar Kabiru Abubakar Bichi ya ce an yi ƙarin ne domin gudanar da wasu ayyuka masu matuƙar muhimmanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban kwamitin kasafin kuɗi, Abubakar Kabiru Abubakar Bichi, ya yi magana kan ƙarin Naira biliyan 700 da aka yi a kasafin kuɗin shekarar 2025.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa ƙarin ya samo asali ne sakamakon janye tallafin kiwon lafiya da Amurka ke bayarwa, da kuma buƙatar gudanar da muhimman ayyukan ci gaba a Najeriya.

An kara N700bn a kasafin kudin shekarar 2025
Abubakar Bichi ya yi karin haske kan karin N700bn a kasafin kudin 2025 Hoto: @HouseNGR, @OfficialABAT
Asali: Twitter

Hon. Abubakar Bichi ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisar Wakilai sun fara tattake wuri kan kudirin harajin Tinubu, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Alhamis ne dai majalisar wakilai ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2025, wanda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar.

Meyasa aka ƙara kasafin kuɗin 2025?

Hon. Abubakar Bichi ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta dakatar da tallafin kiwon lafiya ga ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya.

Ya ce hakan ne ya sanya gwamnati ta ware ƙarin kuɗaɗe domin tallafawa ɓangaren lafiya.

A cewarsa, shugaban ƙasa ya buƙaci ƙarin dala miliyan 200 (kimanin Naira biliyan 300) domin tallafawa shirye-shiryen kiwon lafiya da suka shafi cutar tarin fuka (TB), HIV, zazzaɓin cizon sauro da cutar shan inna.

Ya ƙara da cewa ɓangaren zartarwa ya gabatar da buƙatar neman Naira biliyan 340 domin ɓangaren lafiya da sauran sassa masu muhimmanci.

"Idan aka haɗa, adadin kuɗin yana kusa da Naira biliyan 640."

- Abubakar Kabiru Abubakar Bichi

Sannan ya ce wasu hukumomin gwamnati, da suka haɗa da INEC, NFYU, DSS, da sauransu, sun gabatar da buƙatunsu wanda hakan ya sanya aka ƙara yawan kasafin da Naira biliyan 700.

Kara karanta wannan

Majalisa ta damu da rashin tsaro a Borno, ta ba gwamnatin tarayya shawara

Abubakar Bichi ya jaddada cewa ƙarin kasafin zai taimaka wajen rage gibin kuɗin manyan ayyuka da ake fuskanta a Najeriya, wanda a halin yanzu ya kai Naira tiriliyan 23.

Ya ce ƙarin kuɗaɗen za su taimaka wajen ayyukan gina layin dogo, gina hanyoyin mota, bunƙasa harkar noma da tallafawa ɓangaren ilmi.

Ina za a samo kuɗin a kasafin 2025?

Dangane da damuwar da wasu ke nunawa kan inda kuɗaɗen za su fito, Abubakar Bichi ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnati ta yi nazari sosai kan hanyoyin samun kuɗin shiga kafin amincewa da ƙarin kasafin.

“Kafin ɗaukar wannan mataki, mun gana da ma’aikatar kuɗi, hukumar kwastam da hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa (FIRS).
"Sun tabbatar mana cewa za su iya samar da isassun kuɗaɗe da za su cike wannan ƙarin da aka samu a kasafin kuɗin."

- Abubakar Kabiru Abubakar Bichi

Ɗan majalisa ya yi magana kan ƙudirin haraji

Kara karanta wannan

Mummunar rigima ta kaure tsakanin ƙungiyoyi 2 kan 'kuɗi', an kashe mutane sama da 10

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Gwoza/Damboa, Ahmed Jaha ya bayyana kura-kuran da ya hango a ƙudirin haraji.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa akwai ɓangarori da dama na ƙudirin da suke buƙatar a yi musu gyara kafin a amince da shi ya zama doka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel