'Suna Murna Kamar Sun Cafke Bello Turji,' Farfesa Yusuf kan Yadda Aka Kama Shi

'Suna Murna Kamar Sun Cafke Bello Turji,' Farfesa Yusuf kan Yadda Aka Kama Shi

  • Tsohon Shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf, ya bayyana yadda hukumar EFCC ta kama shi da tsare shi ba tare da sammaci ba
  • Farfesa Yusuf ya yi magana ne bayan da aka gurfanar da shi a gaban kotu, inda aka umarce shi da zama a gidan gyaran hali na Kuje
  • Ya bayyana cewa jami’an da suka kama shi suna tsananin farin ciki, yana mai kwatanta lamarin da cafke dan bindiga, Bello Turji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya bayyana yadda jami’an hukumar EFCC suka cafke shi ba tare da wani sammaci ko bayani ba.

Ya ce a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu, 2025, da misalin karfe 6:30 na yamma, yayin da yake shirin karya azumi, wasu jami’an EFCC biyu sanye da bakaken kaya sun shigo gidansa a Abuja.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Farfesa Yusuf
Farfesa Yusuf ya fadi yadda aka kama shi. Hoto: Muhammad Kime
Asali: Facebook

Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ne ya wallafa bayanin da Farfesa Yusuf ya yi a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Farfesa Yusuf, jami'an EFCC sun bayyana cewa an umarce su da su kai shi hedikwatar hukumar, amma ba su gabatar da wata takardar kama sa ba.

'Suna murna kamar sun kama Turji' - Farfesa Yusuf

Bayan an tasa keyarsa cikin motar EFCC, ya lura da yadda jami’an suka rika farin ciki, kamar sun cafke wani babban dan ta’adda.

Daily Trust ta wallafa cewa ya bayyana yadda matukin motar ke tafiya da cewa:

"Direban ya rika gudu cikin tashin hankali, yana bin hanyoyin da ba daidai ba,"

Farfesa Yusuf ya kara da cewa:

"Jami’an EFCC da ‘yan sandan da ke cikin mota suna ta tafawa da farin ciki, kamar dai sun cafke Bello Turji."

Kara karanta wannan

Yadda Farfesa Yusuf ya ragargaji Tinubu kan alaka da Faransa kafin a kama shi

Ya kara da cewa, duk da irin yanayin da aka jefa shi, bai ji tsoro ko fargaba ba, sai dai ya damu da iyalansa, musamman ‘yarsa mai shekara 14 da ta shaida lamarin.

Menene ya faru a hedikwatar EFCC?

Bayan isarsu ofishin EFCC, Farfesa Yusuf ya ce an kai shi ofishin shugaban sashen binciken almundahana, aka mika masa wasu takardu da aka ce tuhumar da ake yi masa na cikinsu.

Daga nan ya ce aka kai shi dakin kulle mutane, inda ya tarar da wasu mutum uku da aka tsare tare da shi.

Ya ce washe gari da safe, an sanar da shi cewa za a kai shi kotu. Sai dai kafin hakan, jami’an EFCC sun dauke shi hoto a cikin yanayi mara kyau.

"Sun bar ni da kayan da aka dauke ni da su tun daga gida, ba takalmi, ba hula, domin kawai a bata mani suna a idon jama’a,"

Kara karanta wannan

Kotu ta zauna kan shari'ar Farfesa Yusuf, ta ki amincewa da buƙatar beli kan wasu dalilai

- Farfesa Yusuf

An tsare Farfesa Usman Yusuf a Kuje

A ranar Litinin, 3 ga watan Fabrairu, 2025, an gurfanar da shi a gaban kotu, inda alkalin kotu ya dage sauraron karar zuwa 12 ga watan Fabrairu.

Bayan an sake zaman kotun, ba a ba da belinsa ba. Hakan ya sa aka kai shi gidan gyaran hali na Kuje domin ci gaba da tsare shi.

A cewarsa, a gidan yari ya hadu da matasa da dama da ke tsare na tsawon shekaru ba tare da an yanke musu hukunci ba.

"Da yawa daga cikinsu sun shafe fiye da shekara 10 suna jiran shari’a. Lamarin yana da matukar tayar da hankali,"

- Farfesa Yusuf

Kiran Farfesa Yusuf ga 'yan Najeriya

A karshe, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ki yarda da abin da ya kira mulkin danniya, inda yace:

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya yi kokuwa da soja domin kwace bindiga a cikin daji

"Ba zan bari su sa ni yin shiru ba. Zan ci gaba da fadin gaskiya, kuma ba zan yarda da danniya ba,"

Ya kuma gode wa duk masu nuna masa goyon baya, yana mai cewa yana da kwarin gwiwar samun adalci a kotu.

Me yasa aka kama Farfesa Yusuf?

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar Inshora ta kasa NHIS, Farfesa Yusuf ya yi karin haske kan dalilin kama shi.

Farfesa Yusuf ya ce akwai maganganu da ya yi a taron matasan Arewa da ya gudana a jihar Bauchi wanda yana tunanin su ne suka sanya kama shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel