'An Ware Mu': Malaman Musulunci Sun Bukaci Tinubu Ya Yi Duba kan Nadin Mukamai
- Kungiyar Malaman Musulunci ta koka kan rashin adalci wajen nade-naden muƙamai a gwamnatin Bola Tinubu, musamman a Kudu maso Yamma
- Malaman Yarbawa sun bukaci a kafa Kotun Shari’a a yankinsu domin warware shari’o’in da suka shafi Musulmi, bisa tsarin doka da al’adan Najeriya
- Malaman sun jaddada cewa bai kamata kotunan dokokin gama gari su zama zabin tilas ga Musulmi ba, musamman a shari’o’in da suka shafi addininsu
- Wannan na zuwa ne yayin da shirin kafa kotunan Shari'ar Musulunci ya samu tasgaro daga wasu ɓangarori a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ikeja, Lagos - Kungiyar Malaman Musulunci na Yarbawa (CYMSN) tare da Majalisar Shari’a ta Najeriya (SCSN) ta koka kan ware Musulmi a mukamai.
Kungiyoyin sun yi korafi ne kan karancin nade-naden Musulmi daga Kudu maso Yamma a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Malaman Musulunci sun tura bukata ga Bola Tinubu
Shugaban SCSN, Sheikh AbdurRasheed Hadiyatullahi da Shugaban CYMSN, Sheikh Abdurrasheed Mayaleeke su suka bayyana a cikin wata sanarwa, cewar The Guardian.
Kungiyoyin sun kuma nemi a kafa Kotun Daukaka Kara ta Shari’a don warware shari’o’in da suka shafi Musulmi a yankin.
Sun bayyana Kotunan Shari’a ba su shafi shari’o’in da ba na Musulmi ba kamar yadda ake zato.
Malamai sun bukaci damawa da Musulmai a gwamnati
Har ila yau, sun roki Tinubu da ya tabbatar da adalci ga Musulmin Kudu maso Yamma a nade-naden siyasa.
Malaman sun ce tun bayan darewar gwamnati a ranar 29 ga Mayu, 2023, Musulmin Kudu maso Yamma suna fama da wariya duk da goyon bayansu ga Tinubu.
Sun koka kan rashin adalci da rashin damarmakin shiga harkokin ci gaban kasa duk da jajircewarsu wajen nasarar zaben da aka gudanar a 2023.

Kara karanta wannan
2027: Limami ya fadi abin da za a yiwa ƴan siyasar da ke sukar shari'ar Musulunci
An bukaci Ministoci su kare Tinubu
A wani labarin, wasu ministocin Arewa sun fara fitowa fili don kare gwamnatin Bola Tinubu daga sukar da ‘yan adawa da wasu manyan ‘yan siyasa ke yi masa.
Tuni wasu majiyoyi suka ce an ba ministocin umarnin yin duk abin da ya dace domin kare mai gidansu daga zage-zagen yan adawa.
Wasu jiga-jigan siyasa daga Arewa suna takun saka kan inda shugabancin APC zai koma bayan 2027, yayin da ake fafutukar kare karfin Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
