Gwamnatin Tinubu Ta Yi Bayani a kan Daidaita Farashin Abinci

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Bayani a kan Daidaita Farashin Abinci

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta shirya za ta zuba jari mai yawa a aikin gona domin kara yawan samar da abinci
  • Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya ce wannan bangare ne na matakan da ake dauka don rage farashi
  • Sai dai ya ce babu wani shiri da ake da shi na kayyade farashin kayayyakin abinci, domin hakan zai iya matsa wa 'yan kasuwa
  • Ya kara da cewa samun wadatar abinci daga gonaki zuwa kasuwanni, shi ne abin da zai yi raga-raga da farashin kayan abinci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya na rage farashin kayan abinci a kasar nan.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya yi dabarar sanya Tinubu kashe Naira biliyan 33 a aikin titi

Ya bayyana cewa ana shirin cimma hakan ta hanyar zuba jari mai yawa a bangaren aikin gona domin kara yawan amfanin gona da kuma samar da abinci mai yawa a kasuwanni.

Tinubu
Gwamnati ta yi alkawarin daidaita farashin abinci Hoto: @HMMohammedIdris
Asali: Twitter

Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Ministan ya yi wannan bayani ne a Abuja, yayin taron manema labarai don kaddamar da zaman gabatar da ayyukan ministoci na shekarar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan farashin abinci

Alhaji Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin ba za ta tilasta a kayyade farashin kayan abinci ba, domin bin tsarin tattalin arzikin kasuwa mai cin gashin kansa.

Sai dai ya jaddada cewa gwamnati za ta maida hankali kan kara samarwa da yawan amfanin gona domin rage farashin kayan abinci.

Ya ce:

"A baya, muna da kwamitocin kayayyaki da aka kayyade masu farashi, amma a yanzu, domin bin tsarin kasuwa da karfafa gwiwar ‘yan kasuwa, musamman a fannin aikin gona, gwamnati ba ta ga ya zama dole ta fara sanya ido kan farashi ba."

Kara karanta wannan

Sauƙi ya ƙara bayyana da musulmi suka fara shirye shiryen azumin watan Ramadan

Yadda gwamnati za ta rage farashin abinci

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana mayar da hankali wajen tabbatar da cewa an samar da isasshen abinci ta hanyar noma mai yawa don wadata ko ina da abinci.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a ya kara da cewa, idan aka samu abinci a wadace, farashin zai ragu da kansa saboda wadatar abinci a kasuwanni.

Gwamnatin Neja za ta karya farashin abinci

A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa za ta samar da tallafi domin rage farashin kayan abinci yayin azumin watan Ramadan da ke kusanto wa.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Neja, Balogi Ibrahim, ya ce gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa gwamnati za ta fitar da tsare-tsare da za su rage tsadar kayan abinci don saukaka wa talaka.

Gwamna Bago ya bayyana cewa jihar Neja ta samu babbar nasara a harkar noma, inda aka girbi sama da ton miliyan 1 na masara a shekarar da ta gabata, kuma za a yi amfani da kamfanin jihar don daidaita farashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.