Bello Turji Ya Yi Sanyi: Wasu Bakin 'Yan Bindiga Sun Kafa Sabon Sansani a Zamfara

Bello Turji Ya Yi Sanyi: Wasu Bakin 'Yan Bindiga Sun Kafa Sabon Sansani a Zamfara

  • Al’ummar Kuryar Madaro a Zamfara sun koka kan bullar wani sabon sansanin ’yan bindiga ƙarƙashin jagorancin wani 'Dan Sa’adi
  • Duk da ƙoƙarin jami’an tsaro, 'Dan Sa’adi na tattara sababbin mahara da kafa sansanoni a kusa da al’ummomi, yana sake kai hare-hare
  • Mazauna yankin sun bukaci gwamnati ta dauki karin matakan tsaro don murkushe ’yan bindigar da ke sake dawo wa kusa da su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Al’ummar Kuryar Madaro a karamar hukumar Kauran Namoda sun koka kan sabon sansanin da ’yan bindiga suka kafa.

Mazauna wannan gari, sun yi ikirarin cewa 'yan bindiga sun kafa sansanin ne ƙarƙashin jagorancin wani ɗan ta'adda mai suna 'Dan Sa’adi.

Mazauna Zamfara sun koka yayin da aka samu bullar sabon sansanin 'yan ta'adda a jihar.
Wani hatsabibin dan ta'adda ya kafa sabon sansanin 'yan bindiga a jihar Zamfara. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Mutanen garin sun ce duk da ƙoƙarin jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya, 'Dan Sa’adi na ci gaba da kai hare-hare ba tare da sassauci ba, inji rahoton BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kafa sabon sansani a Zamfara

Wani mazaunin yankin ya ce 'Dan Sa’adi na ɗaukar sababbin mutane da kuma tattara ‘yan bindiga da aka tarwatsa domin sake kaddamar da hare-hare.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Yanzu haka wasu baƙin ƴan bindiga ban da wanda muke da su, suna kafa sabbin sansanoni, wani Ɗan Sa'adi ne yake jagorantarsu, kusan ya mamaye ko ina saboda yadda yake daukar mutane, yana karɓar maƙudan kuɗaɗe."

Mazauna yankin sun ce suna cikin matsanancin hali sakamakon yadda ’yan bindiga suka yi wa yankinsu kaka-gida, duk da jajircewar jami’an tsaro.

"Mutanen nan sun matsa mana iya matsi, suna kafa sabbin sansanoni, duk wanda ke yankin nan babu wanda bai san shi ba, kuma jami'an tsaronmu na iya bakin ƙoƙarinsu," inji wani.

Zamfara: Mazauna Kuryar Madora na cikin damuwa

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar Fansar Yamma, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi, kan wannan sabon sansani ya ci tura, duk da tura masa sako.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Kano ta runtuma kora a ma'aikatar shari'a, an samu karin bayani

A kwanan nan, rahotanni daga Zamfara sun ce jami’an tsaro na samun gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ’yan bindiga a jihar.

Sai dai mazauna Kuryar Madaro na nuna damuwa kan dawowar sabbin mahara a yankinsu, suna masu cewa abin na buƙatar karin matakan gaggawa daga gwamnati.

Bello Turji ya yi sanyi a kai hare-hare

A wani labarin, mun ruwaito cewa, matsin lamba daga sojojin Najeriya ya tilasta Bello Turji yin sanyi a kai hare-hare kamar yadda ya saba.

Tsananin azabar da sojoji ke ganawa dan ta'addar ya sa Turji da amininsa tserewa zuwa wata maboyar da har yanzu ba a kai ga ganowa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com