Shahararrun 'Yan Bindiga Sun Tuba, Sun Mika Makamansu ga Jami'an Tsaro

Shahararrun 'Yan Bindiga Sun Tuba, Sun Mika Makamansu ga Jami'an Tsaro

  • Wasu shahararrun ƴan bindiga sun miƙa wuya ga jami'an tsaro a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Ƴan bindigan waɗanɗa suka addabi yankunan Batsari, Safana da Jibia sun bayyana cewa sun tuba daga ayyukan ta'addanci
  • Sun miƙa ƙoƙon bararsu ga gwamnati kan ta samar musu da abin dogaro da kai da ababen more rayuwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Wasu shahararrun ƴan bindiga da suka daɗe suna addabar Batsari, Safana, da Jibia, a jihar Katsina, sun miƙa wuya tare da ajiye makamansu.

Ƴan bindigan sun miƙa wuya ne bayan da sojojin Najeriya suka addabe su da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa.

'Yan bindiga sun tuba a Katsina
Shahararrun 'yan bindiga sun ajiye makamansu a Katsina Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun tuba a Katsina

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

"Ba ku da tabbas": Gwamna ya ja kunnen mukarraban gwamnati, ya ba su shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin ƴan bindigan da suka miƙa wuya akwai Abu Radda, Umar Black, Abdullahi Lankai, Jijjige, da Dabar Musa Dan Gandu, waɗanda ke aiki a yankin Jibia.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ci gaba da kai farmakin da sojoji ke yi a yankin ne ya tilasta wa ƴan bindigan neman zaman lafiya da ajiye makamansu da kansu.

Wace buƙata suka nema wajen gwamnati?

Tubabbun ƴan bindigan sun roƙi gwamnati da ta tallafa musu da hanyoyin dogaro da kai, inda suka buƙaci a gina musu kasuwanni, asibitoci, da samar da ruwan sha mai tsafta don su samu damar dawowa cikin al'umma.

Miƙa wuyan ya samu goyon bayan ƙungiyar (NCSOSACK), ƙarƙashin jagorancin Kwamared Hamisa S. Batsari, wacce ke wakiltar al'ummomin da abin ya shafa a tattaunawar zaman lafiya.

Ƴan bindigan sun miƙa makamansu ga jami'an tsaro tare da sakin wasu mutanen da suka yi garkuwa da su.

Sun kuma sha alwashin barin ayyukan ta’addanci gaba ɗaya tare da rungumar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi wa 'yan binɗiga kofar rago, sun hallaka miyagu

Sojoji za su ci gaba da farmakar ƴan bindiga

Wani babban jami'in soja ya bayyana cewa, duk da miƙa wuyan da tsagerun suka yi, hakan ba zai hana a ci gaba da kai hare-hare ga sauran ƴan bindigan da ba su tuba ba.

Ya ce sojoji za su ci gaba da kai hare-hare sai an tabbatar da cikakken zaman lafiya a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, da sauran yankunan Arewacin Najeriya.

Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan fashi da makami ne sun yi jami'an ƴan sanda guda biyu kisan gilla a jihar Yobe.

Ƴan fashin sun kashe jami'an ƴan sandan ne a ƙaramar hukumar Fune ta jihar Yobe a yayin da suke kan bakin aikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng