Ana Zargin Gwamna Ya Ɗirkawa Fitacciyar Jaruma Ciki a Najeriya, Gaskiya Ta Bayanna

Ana Zargin Gwamna Ya Ɗirkawa Fitacciyar Jaruma Ciki a Najeriya, Gaskiya Ta Bayanna

  • Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya musnata raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya yi wa jarumar shirin BBN, Nengi Hampson ciki a ɓoye
  • A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, ya ce babu kanshin gaskiya a jita-jitar da mutane ke yaɗawa a kafafen sada zumunta
  • Domin kawo karshen zancen, tun farko, taurariyar ta musanta labarin, tana mai cewa ba ta ɗauke da juna biyun wani gwamna a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya karyata jita-jitar da ake cewa shi ne ya ɗirkawa fitacciyar ‘yar shirin 'Big Brother Naija', Nengi Hampson, ciki.

Gwamna Douye Diri ya bayyana labarin da ake yaɗawa a matsayin ƙarya mara tushe da wasu suka ƙirƙira da nufin ɗauke masa hankali daga harkokin shugabanci.

Kara karanta wannan

Halin wasu gwamnoni ya ƙara fitowa, NLC ta koka kan zaman da suke yi a Abuja

Gwamna Diri.
Gwamnan Bayelsa ya musanta jita-jitar da ake cewa ya dirkawa jarumar BBN ciki Hoto: Douye Diri, Nengi Hampson
Asali: Facebook

Jarumar BBN ta fito ta bayyana gaskiya

A wani sako da ta wallafa a shafinta na X, jarumar BBN, Nengi ta tabbatar da cewa tana ɗauke da juna biyu amma ta musanta cewa mai girma gwamna ne ya mata cikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Litinin da ta gabata ne jita-jitar ta bazu a kafafen sada zumunta cewa Gwamna Diri ne ya yi wa jarumar ƴar shekara 26 cikin da take ɗauke da shi.

Da take bayyana gaskiya kan lamarin, Nengi Hampson ta ce:

"Duk da ba ni da lokacin ƙarerayin soshiyal midiya amma na fahimci mun shigo wani zamani da mutane ke yaɗa ƙarya mara kan gado, bari na faɗa maku gaskiya, ba na ɗauke da cikin kowane gwamna."
"Na yi wannan magana ne ba wai don ana ƙoƙarin ɓata ni ba, sai don taɓa mutanen da nake girmamawa, ba zan yarda a canza kyakkyawan labarin rayuwata zuwa wani abu mai muni ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa gwamnatin Tinubu shagube a kan batar da kasafin kudi

"Yayin da nake ci gaba da harkokin rayuwata da rainon cikina cikin farin ciki, ina yi maku fatan alheri da murnar zagayowar ranar masoya da ke tafe.

Gwamna Diri ya musanta jita-jitar

Dangane da wannan batu, hadimin Gwamna Douye Diri kan harkokin soshiyal midiya, Samuel Oredipe, ya karyata jita-jitar, yana mai cewa karya ce da aka shirya ta siyasa.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook a daren Litinin, mai magana da yawun gwamnan ya jaddada cewa babu wata alaka ta musamman tsakanin Jaruma Nengi da Gwamna Diri.

“Labarin da ke yawo game da Nengi da Gwamna Diri ba gaskiya ba ne, Nengi Rebecca Hampson ba ta da wata alaka ta musamman da gwamnan.
“Muna bakin cikin yadda masu yada jita-jitar suka kauda kai daga irin nasarorin siyasa da gwamnan ke samu. Nengi da kanta ta musanta wannan jita-jita," in ji shi.

Oredipe ya kara da cewa wasu abokan adawar siyasa na gwamnan ne ke kokarin yada wannan labari domin kawar da hankalin jama’a daga ayyukan ci gaba da gwamnan ke aiwatarwa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya fadi nasarorin da aka samu kan 'yan bindiga a jihar

Gwamna Diri ya bi bokaye kafin zaɓe

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Bayelsa ya bayyana cewa ya biya bokaye makudan kudi a kasar Kenya a lokacin da yake neman kujerar gwamna.

Duuye Diri ya ce ya biya wasu yan tsibbu a Kenya $10,000 kimanin N5m a kudin Najeriya a wancan lokacin domin su taimaka masa ya zama gwamna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel