Dangote Ya Yunkuro, Ya Fara Hada Sabuwar Motar Peugeot 3008 GT a Jihar Kaduna

Dangote Ya Yunkuro, Ya Fara Hada Sabuwar Motar Peugeot 3008 GT a Jihar Kaduna

  • Kamfanin Dangote ya fara hada sabuwar Peugeot 3008 GT a masana’antar Kaduna tare da shirin kaddamar da Peugeot Landtrek 4x2
  • Peugeot ya yi suna a Najeriya tun shekarun 1980-1990, kamfanin Faransan ya samar da motoci ga gwamnati, masu kudi da talakawa
  • Sabuwar Peugeot 3008 GT na dauke da injin turbo mai karfin lita 1.6, yayin da Peugeot Landtrek 4x2 ke dauke da inji mai lita 2.4

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Kamfanin hada motocin Dangote Peugeot (DPAN) ya fara hada sabuwar mota kirar Peugeot 3008 GT a masana’antarsa da ke Kaduna.

DPAN ya ce sabuwar Peugeot 3008 GT da kuma shirin kaddamar da Peugeot Landtrek 4x2, na daga cikin dabarun rike matsayinta a kasuwar motocin Najeriya.

Kamfanin hada motocin Dangote (DPAN) ya fara hada sabuwar motar Peugeot 3008 GT
Kaduna: Dangote ya fadi shirye-shiryensa da ya fara hada sabuwar motar Peugeot 3008 GT. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A shekarun 1980 zuwa 1990, Peugeot ya mamaye kasuwar motocin Najeriya, inda ya yi suna wajen samar da motoci ga gwamnati, masu kudi da talaka, inji The Nation.

Kara karanta wannan

MRS: An sauke farashin man fetur a jihohin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya fara hada sabuwar motar Peugeot

Dangote Peugeot na karkashin kulawar gwamnatocin jihohin Kaduna, Filato da Kebbi, tare da hadin gwiwa da kamfanin Stellantis, da kuma kamfanin Dangote (DIL) mallakar Alhaji Aliko Dangote.

Peugeot 3008 GT ta zo da injin turbo mai karfin lita 1.6, wadda ta shiga jerin sauran motocin da ake sarrafawa a masana’antar DPAN da aka bude a Kaduna a shekarun baya.

Cikin motocin da ake kera a yanzu akwai Peugeot 301 sedan da Peugeot 5008, wacce ta yi suna saboda girman cikin ta, kyawun zane, da fasahar zamani.

Shirye-shiryen da Dangote ya ke yi

Peugeot Landtrek 4x2 tana dauke da inji mai karfin lita 2.4 tare da tsarin tuki na RWD, kuma tana daga cikin jerin motocin daukar kaya na Peugeot.

Dangote Peugeot ya kuma bayyana yiwuwar kawo sigar Peugeot Landtrek 4x4 a nan gaba domin kara faɗaɗa zaɓin motocin kasuwanci masu ƙarfi.

Kara karanta wannan

Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

Rahoton BusinessDay ya nuna cewa sababbin motocin da ake samarwa a cikin gida na za su bunkasa masana'antar motoci a Najeriya tare da inganta tattalin arzikin kasa.

Dangote da Peugeot sun cimma yarjejeniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kamfanin hada motocin Peugeot da Aliko Dangote sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar kudi ta sama da N4bn.

A shekarar 2018 ne kamfanin tare da attajirin Afrika suka cimma yarjejeniyar bude kamfanin sarrafa motocin Peugeot a jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel