Kamfanin Dangote zai samawa dinbin Jama’a aiki a Garin Kaduna
Mun samu labari cewa Dangote ya samu lasisin kafa Kamfanin motoci na kirar Peugeot na Kasar Faransa a Najeriya. Za a kafa Kamfanin ne a cikin Arewacin Najeriya domin a samawa jama'a sauki.
Kamfanin Dangote zai samu damar kere-kere da kuma hada motocin Peugeot a Garin Kaduna. An shiga yarjejeniya ne tsakanin Kamfanin Peugeot da Kamfanin Aliko Dangote. Kwanaki Dangote ya saye hannun jari a Peugeot.
KU KARANTA:
Za a kafa Kamfanin na Dangote ne da hanyar Kaduna zuwa Abuja kusa da asalin Kamfanin Peugeot. Alhaji Aliko Dangote ya saye hannun jari na Naira Biliyan 11 a Kamfanin motocin wanda ya sa ya fi kowa kudi a Kamfanin.
Wannan dai na cikin kokarin da Gwamnatin nan ke yi na samawa Jama’a aikin yi a Jihar. Kwanaki wani babba a Kamfanin na Peaugoet Jean-Christophe Quemard ya gana da Shugaban kasa Buhari domin kafa kamfanoni a Najeriya.
Irin su Kamfanin Innoson, Toyota, da Kia da ke cikin kasar za su gamu da kalubale daga Dangote. Dangote dai na kokarin shiga harkar sukari da siminti da gishiri da taki da sauran su. Duk Afrika dai babu Attajiri irin Dangote.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng