Dangote da kamfanin Fijo za su kafa kamfanin hada motoci a Arewa
- Kamfanin kera motoci ya rattaba kwantaragi da wanda yafi kowa kudi a Afirka domin fara - harhada motoci a Kaduna
- Kwantaragin zai kunshi jahohin Kaduna, Jigawa, Kebbi, Katsina and Kano
- Za’a fara harhada motocin ne nan da karshen shekara mai zuwa
Shararren kamfanin hada motocin na fijo da ke Kaduna ya sanya hannu akan wata yarjejeniyar kudi ta sama da Naira biliyan 4 tare babban attajirin nan na Naiyar Afirka Aliko Dangote domin fara kera motoci a kasar nan. Yarjejeniyar wacce ta hada da jihohin Kaduna, Kano, Jigawa, Katsina da kuma Kebbi, za ta fara aikin samar da motocin ne a shekarar 2019.
A yarjejeniyar farko dai za’a ta fara aikin hada motoci guda kimanin guda 3,500 daga shekarar 2019 daga nan kuma adadin zai karu zuwa 10,000.
KU KARANTA: Likafa ta cigaba: Kungiyar Izala (JIBWIS) zata gina katafariyar jami’a a jihar arewa
Da ya ke jawabi akan wannan yarjejeniyar mai baiwa gwamnan jihar Kaduna shawara Jimi Lawal, ya bayyana cewa za'a fara fito da motocin a dukkanin bayan watanni uku, sannan kuma ya tabbatar da cewa a watan Disamba za'a kammala ginin kamfanin baki daya tunda har an samu filin da za ayi aikin.
Idan za'a iya tunawa dai kamfanin na Fijo wanda mallakin turawan kasar faransa ne, ya fara kera motocin fijo samfurin 301, wanda kawo yanzu yana samar da manyan motoci kirar fijo.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng