Mummunar Rigima Ta Kaure tsakanin Kungiyoyi 2 kan 'Kuɗi', an Kashe Mutane Sama da 10

Mummunar Rigima Ta Kaure tsakanin Kungiyoyi 2 kan 'Kuɗi', an Kashe Mutane Sama da 10

  • Faɗa mai muni ya ɓarke tsakanin wasu kungiyoyin asiri a jihar Ribas, an tabbatar da cewa mutum 10 sun rasa rayuwarsu
  • Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa rigimar ta samo asali daga wasu kuɗaɗe da kamfanin mai a yankin ke bayarwa
  • Wata majiya daga yankin ta bukaci gwamnati ta kawo masu agaji, tana mai cewa mutane 19 aka kashe a faɗan kungiyoyin guda biyu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Akalla mutum 10 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu a sabon rikicin kungiyoyin asiri da ya faru da safiyar Lahadi a garin Obelle, karamar hukumar Emohua a jihar Ribas.

A makon da ya gabata, ranar Laraba, wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyoyin asiri ne sun kai farmaki yankin kuma sun kashe mutum bakwai.

Taswirar Ribas.
Rigima ta kaure tsakanin kungiyoyin asiri a jihar Rivers, an kashe mutane akalla 10 Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta samu labarin cewa wannan mummunan lamari ya haddasa fargaba, inda mazauna yankin suka tsere domin tsira da rayukansu.

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin asiri 2 sun gwabza a Ribas

Al’umma na cikin jimamin wannan harin, da safiyar Lahadi ‘yan kungiyoyin asiri biyu da ke gaba da juna suka barke da azababben fada domin gwada karfi.

Punch ta ruwaito cewa kafin wannan rana, ƴan kungiyoyin biyu sun shafe sama da shekaru biyu ba tare da wata takaddama ba a taakaninsu ba.

Bayanan da aka tattaro sun nuna cewa rikicin na Lahadi ya faru ne tsakanin kungiyoyin asiri na Naked Wire da Carol.

Bayan kashe mutum bakwai a ranar Laraba, an ce kungiyar da ta yi hasarar ‘ya’yanta ta kai farmaki a Obelle ranar Lahadi, ta fara farautar ƴan uwan wadanda take zargi da hannu a kisan.

Ana zargin an rasa rayukan mutane 19

Wani mazaunin yankin mai suna Kingsley ya bayyana cewa yayin da daya bangaren ke kai farmaki, bangaren da aka kai wa hari ya fito domin ramuwar gayya.

Mutumin ya ce:

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan APC ya tona sirrin 'sabanin' da ke tsakanin 'yan siyasa

“A ranar Lahadi, ‘yan kungiyoyin asiri sun gwabza fada a garinmu. An kashe mutane da yawa, har da wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
"Harbe-harbe ya yi yawa, wanda ya sa mutane suka fara gudu daga yankin. Akalla mutum 19 suka mutu.
"Kungiya ɗaya ta fito farautar ƴan uwan wadanda suka kashe abokansu. Ba da dadewa ba, dayan bangaren ma ya fito, suka fara musayar wuta. An kashe mutane daga kowanne bangare.

Kingsley ya yi kira ga gwamnati da ta kawo ɗauki, yana mai cewa ƴan asiri na neman tarwatsa mazauna yankin.

Yan sanda sun tabbatar da kisan mutane 10

Da aka tuntube ta, kakakin rundunar ‘yan sandan Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa rikicin ya shafi kwangilar kudade daga wani kamfanin mai.

“Faɗan da ya faru yana da nasaba da rikicin kungiyoyin asiri na Naked Wire da Carol, suna faɗa ne kan kudaden da wani kamfanin mai da ke yankin ke bayarwa.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa gwamnatin Tinubu shagube a kan batar da kasafin kudi

“Akalla mutum 10 aka tabbatar da sun mutu, amma har yanzu ba a kama kowa ba, ana ci gaba da gudanar da bincike," in ji ta.

An kama malamai da ake zargi da bokanci

A wani labarin, kun ji cewa mutane sun kama wasu limaman coci biyu da suke zargin da ayyukan asiri a jihar Ribas.

Matasa, waɗanda suka jagoranci damƙe malaman cocin, sun miƙa su ga ƴan sanda kuma an gano abubuwan ban mamaki a majami'un da suke wa'azi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel