Harsashi Ya Kare wa Dan Bindiga Yana Musayar Wuta da Sojojin Najeriya

Harsashi Ya Kare wa Dan Bindiga Yana Musayar Wuta da Sojojin Najeriya

  • Wani ɗan bindiga da aka kama suna fafatawa da dakarun sojin Najeriya tsakar dare a jihar Zamfara ya yi bayani
  • Rundunar soji ta ci gaba da matsa lamba kan ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, lamarin da ke hana su samun mafaka
  • Shahararren ɗan bindiga, Bello Turji, ya buya, ya daina sakin bidiyoyinsa ko ikirarin cewa yana Shinkafi, a zo a same shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Rundunar sojin Najeriya na cigaba da matsawa ‘yan bindiga lamba a yankin Arewa maso Yamma, musamman a jihohin Zamfara da Sokoto.

Yayin wani samame da aka kai da tsakar dare, wani ɗan bindiga da aka kama ya bayyana cewa alburusai sun kare musu yayin da suka fafata da sojoji.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun firgita, an fara neman gwamnati ta karbi tuban jigo a sansanin Turji

Dan ta'adda
An kama dan bindigar da ya yi musayar wuta da sojoji. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Mai sharhi kan batun tsaro, Zagazola Makama ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na X, aka ji sojoji na yin tambayoyi ga dan bindigar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa hare-haren da sojoji ke kai wa sun sanya ‘yan bindiga cikin tsaka mai wuya, inda suke rasa hanyoyin tserewa.

Wasu daga cikinsu sun mika wuya, wasu na neman tuba, yayin da wasu ke gamuwa da ajalinsu a hare-haren da ake ci gaba da kai wa.

Bayanin dan bindiga da aka kama

A cikin bidiyon, sojojin sun yi daurin goro wa dan ta'addar tare da bindigar da ya ke kai hari ga sojoji.

Dakarun sojojin suna yi masa tambayoyi a kan yadda aka kama shi sai ya ce harsashi sun kare masa a lokacin da suke fafatawa.

Rahotanni sun nuna cewa sojoji sun kai farmakin ne bayan samun sahihan bayanai kan mafakar ‘yan bindiga, inda suka afka musu ba zato ba tsammani.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki masallaci, sun sace limami da masallata

Lamarin ya nuna cewa rundunar soji na ci gaba da fatattakar ‘yan bindiga, tare da hana su samun kayan yaki da kuma wuraren buya.

Sojoji sun rufe hanyoyin ‘yan bindiga

A yayin da dakarun soji ke ci gaba da kai hare-hare, rahotanni sun tabbatar da cewa an rufe duk wata hanya da ‘yan bindiga ke amfani da ita domin tserewa.

Sojojin sun kewaye yankunan da ake zargi suna da sansanonin ‘yan bindiga, domin hana su guduwa ko samun taimako daga abokan aikinsu.

Wannan matakin ya sanya ‘yan bindigar cikin tsaka mai wuya, inda ba su da wata hanya sai dai su mika wuya ko kuma su gamu da ajalinsu.

Bincike ya nuna cewa matakin ya fara haifar da sakamako mai kyau, domin kuwa wasu daga cikin ‘yan bindigar sun fara tuba, yayin da wasu ke fuskantar hukunci a hannun jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

Bello Turji ya shiga tsaka mai wuya

Rahotanni daga yankin Shinkafi sun tabbatar da cewa shahararren ɗan bindiga, Bello Turji, ya buya bayan rusa sansaninsa.

Tun da sojoji suka fara zafafa hare-hare, babu wani sabon bidiyo da Turji ya wallafa, babu kuma wata alama ta cewa yana ikirarin yana cikin yankin kamar yadda ya saba.

Hakan na nuna cewa lamarin ya fi karfinsa, kuma ya kasance cikin matsin lambar sojojin tarayyar Najeriya.

Kanu: Kotu ta dage shari'ar dan ta'adda

A wani rahoton, kun ji cewa kotun tarayya ta dage shari'ar jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Mai shari'a Binta Nyako ce ta jagoranci zaman kotun amma dan ta'addar ya ce sam bai amince da sahihancin zaman da Nyako ta jagoranta ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng