'Yan Ta'adda Sun Firgita, An Fara Neman Gwamnati Ta Karbi Tuban Jigo a Sansanin Turji

'Yan Ta'adda Sun Firgita, An Fara Neman Gwamnati Ta Karbi Tuban Jigo a Sansanin Turji

  • Yayin da rundunar sojojin kasar nan ke ci gaba da kai hare-hare a kan 'yan ta'adda a sassan kasar nan, an fara samun masu kawo kansu don a yi sulhu
  • Wani jigo daga sansanin Bello Turji ya nuna shirin ajiye makamansa bayan ya nemi wani malamin addinin Musulunci da ya taimaka masa
  • Sheikh Murtala Bello Asada, shi ne fitaccen malamin da dan ta'addan ya yi wa magana, kuma an tabbatar masa za a duba lamarin idan da gaske ya ke yi
  • Sai dai duk da wannan, bai hana dakarun kai farmaki sansanonin 'yan bindiga a Katsina, Sakkwato, Katsina da Zamfara ba domin fatattakar miyagu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Ana ci gaba da matsin lamba kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma, lamarin da ke sa wasu daga cikinsu sake tunani kan ayyukan da suke yi.

Kara karanta wannan

'Ku tuba kafin Ramadan': Dan ta'adda ya gargadi al'umma, ya fadi matakin da zai ɗauka

Rahotanni sun nuna cewa wani babban jigo daga sansanin Bello Turji yana nuna shirin ajiye makamansa da daina ta’addanci.

Asada
Dan ta'addan Turji ya nemi Sheikh Asada Hoto: Malam Murtala Bello Asada Sokoto
Asali: Facebook

Mai Sharhi a kan tsaro, Zagazola Makama, a shafinsa na X, ya bayyana cewa wani malamin addinin Musulunci, Malam Murtala Bello Asada, ya gana da wani dan ta’adda daga bangaren Turji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda dan ta’adda ya nemi afuwa

Rahotanni sun ce dan ta’addan ya tuntubi Malam Murtala da kansa, yana mai bayyana shirinsa na tuba da daina ta’addanci tsakaninsa da Allah.

Sai dai Malam Murtala ya tunatar da dan ta'addan yadda wasu damammaki na yin sulhu da suka gabata suka tafi a banza saboda 'yan ta'adda sun yi kememe wajen zubar da makamansu.

Dan ta’adda na son zubar da makamansa

Rahotanni sun ce malamin ya tabbatar wa dan ta’addan cewa idan har da gaske ya ke a wannan karon, za a dauki matakan da suka dace don saukaka masa hanyar sulhu.

Kara karanta wannan

Dabara ta fara ƙarewa ƙasurgumin ɗan bindiga, sojoji sun koma maɓoyar Bello Turji

Duk da wannan ci gaban, dakarun soji ba su dakatar da yaki da ‘yan ta’adda ba, yayin da rundunar soji ta ke ci gaba da kai farmaki a jihohin Zamfara, Sakkwato, da Katsina.

Sojojin sun bayyana cewa ana lalata sansanonin ‘yan bindiga, da kashe wadanda suka ki mika wuya, da lalata cibiyoyin samar musu da kayan aiki.

Gwamnan Zamfara ya magantu kan sulhu

A wani labarin, mun wallafa cewa Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa dole sai 'yan bindiga sun cika wasu sharuda kafin a duba yiwuwar yin sulhu don kawo karshen ayyukansu.

A baya, gwamnatin jihar ta sha bayyana cewa ba za ta yi sulhu da ‘yan ta’adda ba, amma yanzu ta bayyana cewa za ta yi la’akari da tattaunawa ne kawai idan ‘yan ta’addan sun ajiye makamansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel