Girma Ya Fadi: An Sake Gurfanar da Tsohon Minista a Kotu kan Zargin Dirka Wa Yarinya Ciki

Girma Ya Fadi: An Sake Gurfanar da Tsohon Minista a Kotu kan Zargin Dirka Wa Yarinya Ciki

  • An sake gurfanar da tsohon Ministan ayyuka na musamman, Kabiru Turaki SAN, a kotu kan zargin yin auren bogi da lalata
  • Bisa bayanan ‘yan sanda, Turaki ya yaudari wata mata da sunan aure, ya zauna da ita a otal daban-daban har tsawon shekaru
  • Kotun ta bayar da belinsa kan kudi N1m tare da sharadin samun mutane biyu da za su tsaya masa kamar yadda doka ta tanada

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotu ta gurfanar da tsohon Ministan ayyuka na musamman, Kabiru Turaki (SAN) bisa zargin yin auren bogi.

Ana zargin Kabiru Turaki ya yaudari wata mata har ya dirka mata ciki, tuhumar da tsohon ministan ya musanta.

An ba da belin tsohon minista kan zargin yaudara da auren bogi
Tsohon minista, Tanimu Turaki ya musanta zargin yaudara da yi wa wata mata ciki a Abuja. Hoto: Tanimu Turaki.
Source: Facebook

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Tanimu Turaki

The Nation ta ce bayan musanta zargin, Turaki ya musanta zarge-zargenmn inda ya ce ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

'Shi zai iya gyara Najeriya': Dan PDP ya roki Kwankwaso, Obi su hade da Atiku Abubakar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda, ana zargin Turaki da “yaudarar wata mace da sunan aure, zina da kuma barazana,” bisa tanadin sashe na 383, 387 da 389 na Dokar Penal.

An bayyana cewa binciken lamarin ya samo asali ne daga wata korafi da aka shigar a ranar 9 ga Agusta, 2024, zuwa ga Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Abuja.

An jero zargin da ake yi wa Tanimu Tanimu

Cikin takardar zargin, rahoton ya ce:

“Kai, Barista Kabiru Taminu Turaki (SAN), tsakanin Disambar 2014 da Agustan 2016, ka zauna da Hadiza Musa a wani otal mai suna Han’s Place.”
“Haka nan, ka zauna da ita a Ideal Home Holiday, Asokoro, tsakanin Agustan 2016 da Nuwambar 2021.”
“Daga nan kuma, ka kama mata wuri a Guzape, daga Nuwamba 2021, inda ka sa ta yarda cewa kun yi aure, kuma kuna tare da ita har ta haifa ‘yar diya.”

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

“Daga bisani, ka yi watsi da ita da ‘yarta daya tilo, ka kuma musanta cewa kai ne mahaifin yarinyar. Haka nan, ka yi barazanar amfani da matsayinka don halaka su, saboda haka, ana zarginka da aikata wadannan laifuka.”

An ba da belin Tanimu Turaki bisa ka'idoji

Bayan an gurfanar da shi, lauyan masu kara, Chijioke Okorie, ya bukaci kotu ta sanya ranar fara shari’a.

Lauyan Turaki, A. I. Mohammed, bai yi gardama ba kan haka, amma ya nemi kotu ta bayar da belinsa, yana mai cewa zai kasance a kotu a duk lokacin da ake bukatarsa.

Mai Shari’a Jega ya bayar da belin Turaki kan kudi N1m tare da mutane biyu da za su tsaya masa domin cika ka'idojin da suka dace.

Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 11 ga Maris din 2025 don ci gaba da sauraran karar da ake yi shekaru da dama.

An zargi Turaki da badakalar makudan kudi

A baya, kun ji cewa ana zargin tsohon Minista, Kabiru Tanimu Turaki da ya rike mukamin a lokacin mulkin Goodluck Jonathan da badakalar kudi.

Kabiru Turaki wanda ya nemi takarar shugaba kasa a 2015 ya taba rike Ministan kwadago, kuma ya na cikin jagororin jam'iyyar PDP a fadin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.