Kiristocin Arewacin Najeriya sun yi wa Kabiru Turaki mubaya’a

Kiristocin Arewacin Najeriya sun yi wa Kabiru Turaki mubaya’a

Manyan Malaman addinin Kirista da ke Arewacin Najeriya da ke da jama’a har a irin su Kasar Amurka da Taiwan sun nuna cewa za su marawa tsohon Minista Kabiru Tanimu Turaki bayan zama Shugaban kasa a zaben 2019.

Kiristocin Arewacin Najeriya sun yi wa Kabiru Turaki mubaya’a
Majalisar Kiristocin Arewa sun goyi bayan Kabiru Turaki yayi takara

Majalisar Kiristocin da ke Arewacin Najeriya sun yi wa Kabiru Taniumu Turaki SAN mubaya’a ne wajen wani taron da aka saba yi duk shekara. Tanimu Turaki yana cikin manyan Ministoci a lokacin Shugaban kasa Jonathan.

Bishof David Ina DD wanda shi ne Jagoran Kiristocin ya aikawa ’Dan takarar Shugaban kasar takarda inda su ka nuna cewa su na goyon bayan sa 100-bisa-100 a 2019 saboda yana da halayen da su ka cancanta ga mai mulki.

KU KARANTA: Mutanen da su ke shirin fitowa takarar Shugaban kasa daga Arewa

Kiristocin sun bayyana cewa Kabiru Tanimu mutum ne mai tsantseni da kuma jajircewa tare da riko da abin da ya dace kuma haka yake tun kafin ya zama Ministan kasar. Kungiyar tace za tayi duk abin da ya dace na goya masa baya.

Manyan Kiristocin na Yankin Arewa sun nemi Kabiru Tanimu ya dage wajen ganin ya gina abubuwan more rayuwa tare da kawo gyaran da za su taimaki al’umma gaba daya idan har ya samu damar darewa kan karagar mulkin kasar.

Idan ba ku manta ba kwanan nan Shugabannin Jam’iyyar PDP na Kananan Hukumomi su kace su na bayan tsohon Ministan. Haka kuma dai tsofaffin Ministocin kasar nan su na tare ne da Kabiru Turaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng