Bayan Sace Janar Tsiga, Ƴan Bindiga Sun Sake Kai Hari Katsina, An Kashe Mutane

Bayan Sace Janar Tsiga, Ƴan Bindiga Sun Sake Kai Hari Katsina, An Kashe Mutane

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki yankin Sabuwa da ke Katsina, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da dama
  • 'Yan sandan Katsina sun ce sun yi musayar wuta da 'yan bindigar yayin dakile harin tare da ceton wasu daga cikin wadabda aka sace
  • Wannan na zuwa ne 'yan awanni bayan wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a Tsige inda suka sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - 'Yan bindiga sun kashe mutane biyu kuma sun sace wasu a sabon harin da suka kai Sabuwa da ke jihar Katsina a ranar Alhamis.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta yi musayar wuta da ‘yan bindigar, inda ta ceci mutane 13, amma 'yan bindigar sun tsere da wasu mutanen.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

'Yan sanda sun yi magana da suka dakile wani harin 'yan bindiga a Katsina
'Yan bindiga sun sake kai hari Katsina, sun kashe mutum 2 da sace wasu da dama. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

Kakakin rundunar ‘yan sanda, DSP Abubakar Sadiq, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a daren Alhamis, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Katsina

DSP Abubakar ya ce miyagun dauke da bindigogin AK-47 sun kai hari Maibakko, wani gari a Sabuwa, inda suka sace mutanen garin bayan harbe-harbe.

Sanarwar DSP Abubakar ta ce:

"A ranar 6 ga Fabrairu, 2025, misalin karfe 1:43 na dare, rundunar ta samu kiran gaggawa daga ofishin ‘yan sanda na Sabuwa.
"An sanar da mu cewa 'yan bindiga dauke da bindigogi masu hadari sun kai farmaki Maibakko da ke Sabuwa, inda suke harbe-harbe da sace wasu mazauna garin."

An kashe mutum 2 a harin 'yan bindiga

DSP Abubakar ya ce nan take jami'an 'yan sanda suka isa wurin, inda suka yi artabu da 'yan ta'addar tare da dakile harin.

"Jami'anmu sun yi nasarar ceto mutane 13, amma 'yan ta'addar sun tsere da wasu daga cikin wadanda suka sace."

Kara karanta wannan

Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya

"Mutane biyu sun mutu sakamakon harbin ‘yan bindiga, yayin da wani mutum daya ya samu rauni. An mayar da wadanda aka ceto ga iyalansu."

- DSP Abubakar

DSP Abubakar ya ce rundunar ta dukufa wajen ganin an kubutar da sauran mutanen tare da kama wadanda suka aikata laifin.

'Yan bindiga sun sace Janar Maharazu Tsiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa kimanin 'yan bindiga 100 sun farmaki garin Tsiga da ke jihar Katsina inda suka sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya).

An tattaro cewa ƴan ta'addar sun afka garin Tsiga da ke karamar hukumar Bakori ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare inda suka tafi da tsohon shugaban na NYSC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com