Mai Tsaron Obasanjo, Manjo Janar Jemitola Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce

Mai Tsaron Obasanjo, Manjo Janar Jemitola Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce

  • Manjo Janar Chris Jemitola (mai ritaya) ya rasu bayan ya yanke jiki ya fadi a filin wasan golf na IBB da ke birnin tarayya Abuja
  • Jemitola ya yi aiki a matsayin mai tsaron lafiyar Olusegun Obasanjo daga 2003 zuwa 2007, inda ya nuna ƙwazo da ƙwarewa a aikinsa
  • Rasuwar Jemitola ta girgiza masana harkokin tsaro, inda aka yaba masa bisa gudunmuwar da ya bayar wajen tabbatar da tsaro a kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Manjo Janar Chris Jemitola (mai ritaya), tsohon dogari ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya rasu.

Jemitola ya rasu bayan ya yanke jiki ya fadi a babban filin wasan golf na Ibrahim Badamasi Babangida da ke Abuja a safiyar Alhamis.

Tsohon mai tsaron lafiyar Obasanjo ya mutu a Abuja
Tsohon dogarin Obasanjo, Manjo Janar Jemitola ya rasu a Abuja. Hoto: @Oolusegun_obj
Source: Twitter

Tsohon dogarin Obasanjo ya rasu

Bisa ga bayanai daga iyalinsa, an garzaya da Jemitola asibiti bayan faduwarsa, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

Sai dai kuma har zuwa yanzu babu rahoto daga iyalan ko makusantansa game da musababbin yanke jiki ko kuma mutuwarsa ba.

An rahoto cewa Manjo Janar Jemitola ya yi aiki a matsayin dogari ga Obasanjo daga 2003 zuwa 2007 a lokacin da yake matsayin Kanal.

Kadan daga ayyukan da Jemitola ya yi

Daga baya, Jemitola ya zama daraktan watsa labarai na rundunar tsaro kuma jami'in soja da ke aikin diflomasiyya a ofishin jakadancin Najeriya a Brazil.

Kafin ya yi ritaya, Jemitola ya rike mukamin babban jami'in tsare-tsare (COPP) na rundunar sojojin Najeriya.

A matsayin COPP, Jemitola ya taka rawar gani wajen tsara dabarun tsaro a cikin rundunar sojojin kasar.

An yi alhinin rasuwar Manjo Janar Jemitola

Bayan barinsa aikin soja, ya yi aiki a kamfanin sadarwa na Pinnacle a matsayin babban mashawarci kan harkokin sadarwar soji.

Rasuwarsa ta girgiza al’umma, inda abokan aiki da sojoji ke alhinin rashinsa tare da yabon kwazo da gudunmuwar da ya bayar.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Tinubu ya bayyana babban abin da ya saka a gaba a Najeriya

Har zuwa yanzu, iyalinsa ba su sanar da lokacin jana’iza ba, amma ana ci gaba da mika sakonnin ta'aziyya da girmamawa, musamman daga abokansa.

Tsohon dogarin Jonathan ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon dogarin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Moses Jituboh, ya rasu a jihar Bayelsa bayan fama da rashin lafiya.

Jituboh, tsohon mataimakin sufeta janar na ‘yan sanda, ya rasu yana da shekara 54. Bayan faduwar Jonathan a zaben 2015, ya koma bakin aikinsa na dan sanda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com