Rashin tsaro: Hoton Buratai yana kwasar nishadi yayin buga kwallon 'Golf' ya janyo cece-kuce

Rashin tsaro: Hoton Buratai yana kwasar nishadi yayin buga kwallon 'Golf' ya janyo cece-kuce

- Shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya, Tukur Buratai, ya sha caccaka a Twitter, bayan bayyanar wani hotonsa yana shakatarwarsa

- Wani dan jarida, Jaafar Jaafar, ya wallafa hoton Buratai yana more rayuwarsa wurin wani taron wasan golf a Abuja ranar Asabar, 5 ga watan Disamba

- Duk da halin da Najeriya take ciki, na rashin tsaro, kuma Buratai yayi alkawarin ba zai koma Abuja ba sai yaci galaba a kan BH a watan Afirilu

Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal janar Tukur Buratai, ya sha caccaka a kafafen sada zumuntar zamani bayan an ga hotonsa a wani wurin wasan kwallon golf da aka yi a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, a Abuja, duk da tabarbarewar tsaro da ke kasar nan.

Wani dan jarida, Jafaar Jafaar, ya wallafa hoton shugaban rundunar sojin kasan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya bayyana alhininsa a kan faruwar lamarin.

Kamar yadda ya wallafa, "Shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriya, Buratai yana shakatawarsa a Abuja.

KU KARANTA: Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa

Rashin tsaro: Hoton Buratai yana kwasar nishadi yayin buga kwallon 'Golf' ya janyo cece-kuce
Rashin tsaro: Hoton Buratai yana kwasar nishadi yayin buga kwallon 'Golf' ya janyo cece-kuce. Hoto daga @JaafarSJaafar
Asali: Twitter

KU KARANTA: 2023: Jigo a APC ya bayyana mutanen da za su fitar da yankin shugaban kasa

"Amma a can arewa maso gabas, Boko Haram tana baje kolinta, a arewa maso yamma da kuma tsakiya, 'yan Najeriya suna fama da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane suna amshe 'yan kudadensu.

"Amma a watan Afirilu, Buratai ya ce ba zai koma Abuja ba har sai yaci galaba a kan Boko Haram."

A wani labari na daban, wasu mutane dauke da makamai da ake zargin 'yan bindiga ne sun tarwatsa masu kada kuri'a a kauyen Oroji da ke gundumar Rini ta karamar hukumar Bakura da ke jihar Zamfara a ranar Asabar.

Lamarin ya faru a ranar Asabar yayin da ake zaben maye gurbi na majalisar dattawa, kamar yadda rahoto daga HumAngle ya bayyana.

Jaridar Daily Trust ta bayyana yadda wani mai kada kuri'a mai suna Sulaiman Muhammad, yake sanar da cewa lamarin ya faru wurin karfe 8:30 na safe yayin da ake dab da fara saka kuri'u.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel