Wani Mutumi Sanye da Kayan 'Yan Sanda Ya Saita Bindiga, Ya Harbe Jami'in FRSC

Wani Mutumi Sanye da Kayan 'Yan Sanda Ya Saita Bindiga, Ya Harbe Jami'in FRSC

  • Wani da aka gani sanye da kayan ‘yan sanda ya harbi wani jami’in FRSC yayin wani aikin binciken lambar mota ta bogi a Legas
  • Hukumar FRSC ta dakatar da aikin kaddamar da yaki da lambar mota ta bogi saboda wannan mummunan lamari da ya faru
  • Ba a kai ga tabbatar da cewa wanda ya ko sahihin dan sanda ne ko sojan gona ba, kuma ba a samu jin bayani daga jami'in tsaron ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Wani mutumi sanye da kayan ‘yan sanda ya harbi wani jami’in hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) a jihar Legas.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da jami’an na FRSC reshen Legas ke aikin bincike kan amfani da lambar mota ta bogi.

Wani da ake zargin dan sanda ne ya harbi jami'in FRSC a Legas
Hukumar FRSC za ta yi bincike da wani 'dan sanda' ya harbi jami'inta a Legas. Hoto: @FRSCNigeria
Source: Twitter

Ana zargin dan sanda ya harbi jami'in FRSC

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

Kwamandan FRSC reshen Legas, Kehinde Hamzat, wanda ke jagorantar kaddamar da aikin, ya ki magana kan lamarin, inji rahoton Channels TV.

Sai dai kuma, Kehinde Hamzat ya roki manema labarai da su yi hakuri domin ba shi damar gano musabbabin faruwar lamarin.

Ba a tabbatar ko wanda ya harba bindigar jami’in ‘yan sanda ne ko sojan gona ba yayin da rundunar ‘yan sandan Legas ba ta ce uffan kan lamarin ba.

FRSC ta dakatar da binciken lambar bogi

Hukumar FRSC reshen jihar Legas ta dakatar da kaddamar da shirin yaki da lambar mota ta bogi sakamakon wannan lamarin.

Kehinde Hamzat ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai kan sakamakon da aka gani na kaddamar da shirin a ranar farko.

Ya ce hukumar za ta ci gaba da bibiyar lamarin tare da daukar matakin da ya dace don tabbatar da tsaron jami'anta yayin gudanar da ayyukansu.

Direba ya yi ajalin jami'in hukumar FRSC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani direban babbar mota ya kashe jami’in hukumar kiyaye hadura ta ƙasa (FRSC) a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Tsanyawa/Kunchi: Mutanen Kano sun shafe shekara 1 babu 'dan majalisar dokokin jiha

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin, Idris Hamisu, ya rasa ransa ne yayin da yake kokarin bin umarnin kai motar zuwa ofishinsu.

Direban tare da yaron motarsa sun wurgo jami’in daga cikin motar yayin da suke gudu, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com