Jama'a sun suburbudi jami'in FRSC da ya ja hadari yayin kokarin kama mai laifi (Bidiyo)

Jama'a sun suburbudi jami'in FRSC da ya ja hadari yayin kokarin kama mai laifi (Bidiyo)

Mazauna garin Abuja sun yiwa wani jami'in hukumar kiyaye hadura a hanyoyin Najeriya watau FRSC, dukan tsiya saboda janyo hadarin da yayi a kan titi.

Hakan ya faru ne a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, 2020, kamar yadda TVC ta bayyana.

An bayyana cewa jami'in yana kokarin kama wani mai laifi dake kokarin guduwa ne kuma tsautsayi ya ja aka samu wani sabon hadarin.

Hakan ya yi sanadiyar mumunan lalata motar wani mutumi dake tsaye a bakin hanya.

Kalli bidiyon:

DUBA WANNAN: Duk masu ihun 'Sai Baba' har yanzu munafukai ne, ko Buhari bai iya zuwa Katsina - Sheik Bello Sokoto

A wani labarin, Yan Sanda da ke birnin tarayya Abuja sun kama wani mutum da ya saci mota mallakin hukumar kiyayye haɗɗura ta ƙasa, FRSC, daga hedkwatar hukumar da ke Wuse Zone 5, Abuja.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manzah ya fitar ta ce an kama Hamisu Tukur mai shekaru 25 ne yayin bincike da hukumar ke yi a titi.

"Bayan rahoton da rundunar ƴan sanda ta Abuja ta samu, rundunar a ranar 5 ga watan Satumban 2020 ta kama wani Hamisu Tukur mai shekaru 25 a kusa da Bwari saboda sace wata mota mallakar Hedkwatan hukumar kiyayye haɗɗura ta ƙasa FRSC da ke Sky Memorial, Wuse Zone 5.

"Yan sandan yankin Bwari ne suka cafke wanda ake zargin yayin bincike da suke yi bayan rahoton da hukumar ta FRSC ta shigar wa ƴan sanda.

"An kama wanda ake zargin da mota ƙirar Toyota Hilux HQ-26RS mai launin fari da makulli ƙwara ɗaya.

KARANTA WANNAN: An dakatar da Likitoci biyu kan mutuwar wata jaririya a Asibiti

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel