Naja'atu: El Rufa'i Ya Tono Bayanai kan Zargin Rashawa da Ribadu Ya Yi wa Tinubu a 2006

Naja'atu: El Rufa'i Ya Tono Bayanai kan Zargin Rashawa da Ribadu Ya Yi wa Tinubu a 2006

  • Nasir El-Rufa’i ya goyi bayan kalaman Naja’atu Muhammad kan zargin Nuhu Ribadu da ya taba sukar Bola Tinubu a shekarar 2006
  • Nuhu Ribadu ya musanta zargin, yana mai cewa ba zai lamunci bata masa suna ba tare da bukatar Naja’atu ta bada hujjoji ko ba shi hakuri
  • A nata bangaren, Hajiya Naja’atu ta dage cewa tana da hujjoji kan kalaman Ribadu, tare da kalubalantar shi da ya kai ta kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya bayyana goyon bayansa ga kalaman Naja’atu Muhammad da ke zargin Nuhu Ribadu da yin suka ga Bola Tinubu.

Hajiya Naja'atu Muhammad ta yi magana ne cewa Nuhu Ribadu ya zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da rashawa a lokacin da yake jagorantar hukumar EFCC.

Kara karanta wannan

Rusau: Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki zafi bayan kisan mutum 4

Naja'atu Muhammad
El-Rufa'i ya shiga dambarwar Ribadu da El-Rufa'i. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Nuhu Ribadu|Mohammed Malami
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da El-Rufa’i ya fitar Facebook a yau, ya tabbatar da cewa kalaman Naja’atu gaskiya ne, yana mai cewa akwai bayanan da za su tabbatar da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya ce za a samu bayanan a cikin takardun majalisar zartaswa ta tarayya da kuma rahotannin jaridu na shekarun baya.

Wannan batu ya sake tunzura rikicin siyasa tsakanin manyan jami’an gwamnati da masu fashin baki a Najeriya.

Zargin Nuhu Ribadu da martanin Naja’atu

A cikin wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Hajiya Naja’atu Muhammad ta zargi Nuhu Ribadu da sauya matsayinsa daga mai suka zuwa mai kare shugaba Bola Tinubu.

Hajiya Naja'atu ta ce a lokacin da Nuhu Ribadu ke shugabantar EFCC, ya bayyana Bola Tinubu a matsayin daya daga cikin manyan masu cin hanci da rashawa a Najeriya.

"Amma yanzu kuma yana cikin masu kare shi a gwamnati. Wannan yana nufin ko dai Ribadu ya yi karya a baya ko kuma yana yin karya yanzu."

Kara karanta wannan

"Ina tsaye a kan baka ta," Naja'atu Muhammad ta kalubalanci Nuhu Ribadu ya tafi kotu

- Hajiya Naja'atu Muhammad

Ribadu ya mayar da martani ta hannun lauyansa, Dr. Ahmed Raji (SAN), yana mai cewa bai taba fadin irin wadannan kalamai ba, kuma zargin Naja’atu ya bata masa suna.

Ya bukaci ta janye kalamanta tare da bada hakuri a manyan jaridu guda biyar, ko kuma zai dauki matakin shari’a.

Naja’atu ta dage kan gaskiyar kalamanta

Hajiya Naja’atu ta ki janye kalamanta, inda ta bayyana cewa tana da hujjoji da ke tabbatar da abin da ta fada.

"To me na yi masa da zan ba shi hakuri? Kai ka taba jin mutum ya fadi gaskiya, ya janye?
"Abin duk da na fada, ina tsaye a kan baka ta. Duk wanda ke son gaskiya zai iya duba rahotanni na baya a kafafen yada labarai,"

- Hajiya Naja'atu

Ta kara da cewa akwai bidiyon kalaman Nuhu Ribadu a YouTube da sauran takardu na hukumomin gwamnati da ke tabbatar da zargin da ta yi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Naja'atu: Ribadu ya dauki zafi, ya ba 'yar gwagwarmayar wa'adi kan bata suna

El-Rufa'i ya shiga rikicin Naja'atu da Ribadu

Nasir El-Rufa’i ya tabbatar da sahihancin zargin Naja’atu, yana mai cewa:

"Nuhu Ribadu ya taba fadin wadannan kalamai a shekarar 2006 yayin taron majalisar zartaswa ta tarayya.
"Takardun wannan taro da rahotannin jaridar Daily Trust na watan Fabrairu, 2007, suna dauke da bayanai masu tabbatar da hakan.

A karshe, Nasir El-Rufa'i ya ce musa maganar da Ribadu ya yi akwai alamar yana da cutar mantuwa.

El-Rufa'i ya yi martani ga Uba Sani

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna ya nuna yatsa ga gwamnan Uba Sani kan maganar sabanin da ke tunanin ya na tsakaninsu.

Nasir El-Rufa'i ya yi magana ne bayan gwamna Uba Sani ya ce ba shi da wata matsala da tsohon gwamnan jihar da ya sauka ya ba shi mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel