Rusau: Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Dauki Zafi bayan Kisan Mutum 4
- Majalisar dokokin Kano ta soki kalaman da Shugaban Jami'ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu, ya yi kan rusau a Rimin Zakara
- Majalisar ta bukaci a zurfafa bincike kan yadda aka yi rusau da tsakar dare, wanda ya haddasa mutuwar mutane hudu da raunata wasu
- Hon. Aminu Sa'adu Ungogo ya bayyana cewa dole ne a binciki wadanda suka dauki nauyin wannan aiki tare da daukar matakin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta yi Allah wadai da kalaman shugaban jami'ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu ya yi a kan aikin rusau a Rimin zakara da ya kashe mutane hudu.
A zaman majalisar na ranar Talata, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ungogo a zauren, Aminu Sa'adu Ungogo ya bayyana cewa yadda aka dauko aikin rusau din bai dace ba.

Asali: Facebook
A wani bidiyo da Hon Musayyib Kawu Ungogo ya wallafa a shafin Facebook, an ji yadda dan majalisar ya nanata cewa rai ba abin wasa ba ne, saboda haka dole a zurfafa bincike a kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zargi Shugaban jami'ar Bayero da cewa bai cancanci matsayin da ya ke rike da shi ba, duba da yadda ya ke kalaman da ke kaskantar da ran dan adam.
Majalisar Kano ta soki tsarin rusau
Dan majalisar Ungogo a majalisar dokokin Kano ya bayyana cewa babu inda za a amince da a shiga gidajen jama'a da talatainin dare domin gudanar da rushe-rushe.
Hon Aminu Sa'adu Ungogo ya ce:
"Ashe ba a sani ba, wasu jami'ai ne su ka je, su ka yi wannan aiki, sakamakon haka aka rasa ran mutum hudu,."
"Wasu daga cikinsu, aka ji masu raunuka, har da harbe-harbe, wanda wasu daga ciki yanzu su na nan, a asibiti a kwance ana kula wa da lafiyarsu."
Ya kara da cewa wannan lamari da ya afku abin kaico ne, abin takaici ne, kuma abin Allah wadarai ne.
Majalisa za ta dauki mataki a kan rusau
Hon. Aminu Sa'adu Ungogo ya mika bukatarsa ga majalisar dokokin Kano a kan matakan da za a dauka domin mutunta ran dan adam da tabbatar an yi mutanen Rimin Zakara adalci.
Ya ce:
" Lallai a yi kwamiti a gidan nan wanda zai bincika, kuma ya tabbatar da irin abin da ke wakana, kuma ayi hukunci na gaske a kan wadanda aka zalunta aka kashe su ba-su-ji-ba ba-su-gani-ba a cikin talatainin dare, domin ya saba ka'ida.
"Na biyu, lallai ne a samarwa da wadanda su ka jikkata da wadanda su ka rasa iyalansu madogara a cikin rayuwarsu, yadda za su ci gaba da yin rayuwa cikin sauki, ba da aka kuntata masu.
Dan majalisar ya kuma shawarci gwamna Abba Kabir Yusuf, a kan ya tabbatar an dauki mataki a kan duk wanda aka kama da laifi a rusau da ya gudana a Rimin Zakara.

Kara karanta wannan
"Su na cewa maulidi bidi'a ne," Sarkin Kano ya yi raddi a kan 'Qur'an convention'
Kwankwaso ya shawarci gwamnati a kan rusau
A baya, kun ji cewa kusa a jam'iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce matakin kafa kwamitin binciken rusau da ya yi sanadin mutuwar mutane a Rimin Zakara ya yi kadan.
Ya ce abin da zai dace wa shi ne, gwamna Abba Kabir Yusuf tare da kwamishinonin filaye da ayyuka su ziyarci iyalan mamatan domin yin ta'aziyya, ba da diyya da kuma ba su hakuri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng