"Mu Taya Su da Addu'a": Sanata Goje Ya Lissafa Shugabannin da Ke Son Kawo Ci Gaba
- Muhammad Danjuma Goje ya yabawa shugaba Bola Tinubu da majalisar tarayya bisa kokarinsu na yin shugabanci mai nagarta a kasa
- Tsohon gwamnan ya yi kira ga al’ummar ƙasa da a ci gaba da addu’a don samun nasarar shugabancin Tinubu da 'yan majalisa
- Sanata Goje ya ce majalisar dattawa ta 10 za ta ci gaba da aiki tare da bangaren zartarwa domin ganin an samu ci gaba mai ɗorewa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon gwamnan Gombe, Sanata Mohammed Danjuma Goje, ya yabawa shugaba Bola Tinubu bisa yadda yake jagorancin 'yan Najeriya cikin kwarewa.
Sanata Danjuma Goje ya bayyana hakan ne a Abuja yayin karɓar lambar yabo daga ƙungiyar manema labarai ta majalisar dattawa a ranar Litinin.

Asali: Twitter
Danjuma Goje ya nemi a taya Tinubu da addu'a
Sanata Goje ya ce abin da Najeriya ke buƙata a wannan lokaci shi ne addu’a ga shugabanni da al’umma baki ɗaya don nasarar kasar, inji rahoton Vangaurd.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi addu’a ga shugaba Bola Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima, Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas.
Sanata Goje ya kuma yi addu’a ga ma’aikatan majalisar tarayya da ‘yan jarida da ke watsa dukkanin ayyukansu a kullum don wayar da kan 'yan Najeriya.
Sanata Goje ya kambama majalisar dattawa ta 10
Goje ya ce wannan lambar yabo da aka ba shi tamkar allura ce ta zaburar da shi a kan kara sadaukar da kai wajen yi wa kasa hidima.
Ya bayyana cewa majalisar dattawa ta 10 tana aiki tare da bangaren zartarwa don samar da kyakkyawan shugabanci a Najeriya.
Yayin da ya ce majalisar na aiki tukuru don ci gaban kasa tun bayan kafuwarta a watan Yunin 2023, Sanata Goje ya jaddada muhimmancin taya Tinubu da addu'a.
'Tinubu ya manta da Arewa' - Sanata Goje
A wani labarin, mun rahoto cewa Sanata Danjuma Goje ya kalubalanci gwamnatin Bola Tinubu kan ware wasu jihohin Arewa wajen aiwatar da ayyukanta.
Sanata Goje ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fi mai da hankali kan manyan ayyukan titi a wasu yankunan ƙasar, tana barin wasu a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng