'Yana Jami'a Aji 2': An Fadi Matakin Karatun Rikakken Mai Garkuwa da Mutane da Ya Nemi Afuwa

'Yana Jami'a Aji 2': An Fadi Matakin Karatun Rikakken Mai Garkuwa da Mutane da Ya Nemi Afuwa

  • Lauyan Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya bukaci sassauci ga wanda ake zargin ta garkuwa da mutane
  • Lauyansa mai suna Emefo Etudo, ya bayyana cewa Evans ya tuba, yana karatun jami’a kuma ya kai aji biyu bayan ya samu A1 a jarabawar NECO
  • Kotun ta dage shari’ar zuwa Maris 20, 2025, bayan da lauyan gwamnati ya tabbatar da cewa Evans ya gabatar da bukatar sulhu ga gwamnatin jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ikeja, Lagos - An yanke hukunci kan Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, da ke fuskantar shari'a kan garkuwa da mutane.

Ana tuhumar Evans ne da garkuwa da mutane da kuma karbar biliyoyi na kudin fansa.

An fadi matakin karatun fitaccen mai garkuwa da mutane
Lauyan mai garkuwa da mutane, Evans ya fadi ƙoƙarinsa a bangaren karatu da sakamakon da ya samu. Hoto: Legit.
Asali: Original

Zarge-zargen da ake yi wa Evans

An bayyana hakan ne yayin sake gurfanar da shi a Kotun Babban Birnin Lagos da ke Ikeja, Daily Trust ta tabbatar.

Kara karanta wannan

"Na tuba, ba zan kara ba": Kasurgumin dan ta'adda na so gwamnati ta yi masa afuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi Evans da kisan Peter Nweke da Chijioke Ngozi a ranar 27 ga Agusta, 2013, da misalin karfe 10 na dare a FESTAC, Lagos, cewar Punch.

Evans da abokin aikinsa, Joseph Emeka, sun amince da sake gurfanar da su, amma sun musanta duk tuhume-tuhumen da aka gabatar a kansu.

Lauyan gwamnati, Sule Yusuf ya bukaci kotu da ta ci gaba da tsare su, sannan ya bayyana cewa Evans da abokin aikinsa sun nemi sulhu da gwamnati.

An fadi ƙoƙarin Evans a makaranta

Lauyansa, Emefo Etudo, ya ce:

"Yana matashi da ya fada tarkon aikata laifi, amma yanzu ya tuba, Yana karatu a aji 2 a Jami’ar NOUN."
"A gaskiya, ya samu A1 a duk darussan da ya rubuta a jarabawar NECO yayin da yake gidan yari, wannan ya samu ne ta dalilin tallafin karatu daga Gwamnatin Tarayya."
"Ya kamata a ba shi dama don ya zagaya makarantun Lagos yana fadakar da matasa game da hatsarin aikata laifi."

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ba za ta raga ba," Abba Gida Gida ya zare takobin yaki da rashawa

- Emefo Etudo

Lauyan gwamnati, Sule Yusuf, ya shaidawa kotu cewa an fara sabuwar shari'ar kuma an bukaci sake gurfanar da wadanda ake zargi.

Lauyan Evans, Etudo, ya tabbatar da cewa sun mika bukatar sulhu ga gwamnatin Lagos ta hannun Ofishin Antoni Janar.

Evans ya yi tone tone kan Abba Kyari

Kun ji cewa Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans ya fallasa wasu manyan bayanai dangane da Abba Kyari.

A cewar Evans, Kyari da yaransa sun azabtar da shi a lokacin da ake tsaka da tuhumarsa akan laifin garkuwa da mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel