Yadda Gwamnonin Arewa Su ka Rabu a kan Sulhu da 'Yan Ta'adda

Yadda Gwamnonin Arewa Su ka Rabu a kan Sulhu da 'Yan Ta'adda

Jihohin Arewa sun bayyana ra'ayoyi daban-daban game da tattaunawa da 'yan ta'adda domin yin sulhu don magance matsalar ta'addanci, a gefe guda, masu ruwa da tsaki su ka ba da ta su shawarar a kan batun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - A baya-bayan nan, gwamnan Kaduna, Uba Sani ya jagoranci yin sulhu da 'yan bindiga, wanda ake sa ran zai taimaka wajen sama wa jama'a sauki.

Masu sharhi a kan harkokin tsaro da dama su na ganin akwai bukatar a sake duba na tsanaki a kan batun yin sulhu da 'yan bindiga idan ana son wanzuwar zaman lafiya.

Kaduna
Ra'ayin gwamnonin Arewa a kan rashin tsaro ya bambanta Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda/Uba Sani/Dauda Lawal
Source: Facebook

Legit ta yi duba na tsanaki a kan yadda wasu jihohin Arewa su ka barranta kansu da kokarin sulhu da 'yan ta'adda, yayin da Kaduna ta ce ta fara ganin amfanin hakan.

Kara karanta wannan

Girma ya fadi: An sake gurfanar da tsohon minista a kotu kan zargin dirka wa yarinya ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Zamfara: Matsayar gwamnati a kan rashin tsaro

BBC Hausa ta ruwaito gwamna Dauda Lawal Dare ya sha nanata cewa gwamnatinsa ba za ta taba amince wa da sulhu da bata-garin 'yan ta'adda ba.

Ya yi zargin cewa yin sulhu da 'yan bindiga zai kara tabarbara tsaro, saboda haka ya sha alwashin daukar matakan kare rayukan jama'arsa.

Dauda Lawal
Gwamnan Zamfara ya ce ba zai taba yin sulhu da 'yan ta'adda ba Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Amma a shekarar 2024, an yi zargin gwamnatin ta yi amai ta lashe a kan batun sasanta wa da 'yan ta'adda, inda Sakataren gwamnatin, Malam Abubakar Nakwada ya musanta zargin.

2. Abin da Katsina ke yi kan rashin tsaro

Thisday ta ruwaito matsayar gwamnatin Katsina a kan rashin tsaro, gwamna Umaru Dikko Radda na ganin babu abin da ya dace irin fito-na-fito da 'yan bindiga.

Umaru
Gwamnan Katsina na son a fatattaki 'yan ta'adda Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda
Source: Twitter

Ya sha daukar alkawain taimaka wa dukkanin garuruwan da ke da ra'ayin kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga, inda ya ke ganin za a iya ba matasan garuruwan makamai.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta bullo da sabuwar dabarar kashe bayin Allah, an hallaka mutane a Borno

3. 'Yadda Kaduna ta yi sulhu da 'yan ta'adda

Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya zama gwamna na farko a baya-bayan nan da ya yi sulhu da 'yan bindiga da su ka addabi mazauna jihar.

Duk da sukar matakin da wasu ke yi, gwamnan ya bayyana cewa ba zai zauna ana kashe mutanen da su ka zabe shi ba.

Uba Sani
Gwamnan Kaduna ya yi sulhu da 'yan ta'adda Hoto: Senator Uba Sani
Source: Twitter

Ya bayyana cewa tun bayan da aka yi sulhun, 'yan bindiga sun saki wasu mutane akalla 200 da aka yi garkuwa da su a baya.

Uba Sani ya tabbatar da cewa sun sa ido kan yadda sulhun ke tafiya, sannan akwai tabbacin miyagun ba za su koma ruwa ba.

4. Matsayar sauran jihohin Arewa a kan ta'addanci

Jihohin Sakkwato da Neja da ke fama da rashin tsaro a nan da can ba su fito karara sun kore yiwuwar sulhu da 'yan ta'adda ba zuwa yanzu.

Amma an ji gwamnatocin jihohin su na karfafa wa jami'an tsaro gwiwa a kan su tabbata an kawar da miyagun 'yan ta'addan da su ka hana jama'a sakat.

Kara karanta wannan

"Gwamnati ta yi banza da mu," ASUU ta ce ba a damu da barazanar yajin aikinta ba

Ra'ayin masana a kan sulhu da 'yan ta'adda

Daily Post ta wallafa cewa tsohon kakakin rundunar sojojin kasar nan, Birgediya Janar Sani Kuka Sheka mai ritaya ya bayyana cewa duk da sulhu abu ne mai kyau, amma akwai sarkakiya.

A dogon sakon da ya rubuta, ya bayyana cewa dole ne sai jihohin Arewa sun yi taka tsan-tsan da tuban da 'yan bindiga a yankin ke yi, kar a rika samun tuban muzuru.

A nasa bangaren, Dr. Isma'il Tanko Wudilawa, Shugaban rundunar hadin gwiwa ta JTF mai ritaya, ya bayyana cewa dama a kan magance rashin tsaro da karfin soja ko sulhu.

Ya tabbatar wa Legit cewa abin da gwamnatin Kaduna ta yi abu ne mai kyau matuka, amma dole sai an rika bibiya domin gudun kar 'yan ta'addan su yaudari gwamnati.

'Yan ta'adda sun kai hari Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai hari garuruwa daban-daban a jihar Neja, inda su ka sace mutane sama da 100 a farmakin da su ka kai.

Kara karanta wannan

Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya

Ɗan Majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar Rafi, Hon. Zubairu Isma'il Zannah ne ya tabbatar wa takwarorinsa hakan a zaman majalisa, inda aka ba da shawara ga gwamnati don shawo kan lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng