Jigawa: Gwamna Zai Ciyar da Mabukata 189, 000 a Ramadan, An Ji Kudin da Zai Kashe
- Gwamnatin Jigawa za ta ciyar da mabukata 189,000 a watan Ramadan, inda za ta kashe Naira biliyan 4.8 don aiwatar da shirin
- Kwamishinan watsa labarai ya ce za a samar da nau'ikan abinci uku a cibiyoyi 630, inda kowacce cibiya za ta ciyar da mutum 300
- Har ila yau, gwamnatin ta amince da gyaran asibitoci 114 a fadin jihar, wanda zai lakume Naira biliyan 9.7 don inganta kiwon lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta shirya ciyar da mabukata 189,000 a watan azumin Ramadana na wannan shekarar ta 2024.
Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatin ke daukar nauyin ciyar da mabukata a lokacin Ramadana ba, ko a 2024 ta yi hakan.
Ramadan: Za a ciyar da mutane 189,000 a Jigawa
A watan azumin bana, Gwamna Umar Namadi ya amince a kashe N4.8bn domin gudanar da shirin ciyar da mabukata 189,000 a fadin jihar, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar gwamnatin jihar, wannan shirin zai tallafawa mabukata da marasa galihu a cikin watan azumin mai falala.
Kwamishinan watsa labarai, Sagir Musa ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a daren ranar Litinin.
Sagir Musa ya yi magana ne jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar Jigawa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
Yadda tsarin ciyarwar Ramadan zai kasance
A cewar kwamishinan, gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar kananan hukumomi ne za su samar da kudin da za a gudanar da shirin.
Sagir Musa ya bayyana cewa jihar za ta samar da kaso 55% na kudin da ake bukata yayin da kananan hukumomin za su samar da ragowar kaso 45%.
Ya kuma bayyana cewa an kara adadin cibiyoyin da suke dabafawa da kuma raba abincin daga 609 na shekarar 2024 zuwa 630 a bana.
Kwamishinan ya kara da cewa dukkanin cibiyon 630 za su rika samar da nau'ikan abinci guda uku ga duk mutum daya a kowacce rana.
"Majalisar ta amince a rika dafa abinci kala uku, da ya hada da kunu, kosai da kuma shinkafa dafa-duka, inda kowacce cibiya za ta ciyar da mutane 300."
- Sagir Musa.
Gyaran asibitoci 114 zai lakume N9.7bn
Kari a kan shirin ciyarwar, majalisar zartarwar jihar ta amince da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya na gundumomi guda 114 da ke a fadin jihar.
Wannan aikin zai lakume Naira biliyan 9.7, kuma zai taimaka wajen bunkasa harkar kiwon lafiya a jihar bisa tsarin kiwon lafiya na duniya.
Kwamishinan ya bayyana cewa aikin sabunta asibitocin ya na karkashin shirin bankin duniya na rigakafi da yaki da cutar zazzabin cizon sauro.
"Aikin sabunta cibiyon kiwon lafiyar ya nuna jajurcewar gwamnatin jiha na inganta kiwon lafiyar al'ummar Jigawa baki daya."
- Kwamishinan watsa labaran Jigawa.
Gwamnoni 7 sun kashe N28.3bn a Ramadan 2024
A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla jihohi bakwai a Najeriya suka kashe Naira biliyan 28.3 wajen aiwatar da shirin ciyar da mabukata a watan azumin 2024.
Kididdiga ta nuna cewa jihar Katsina ta fi sauran jihohi kashe kuɗi, inda ta kashe kimamin Naira biliyan 10, yayin da jihar Yobe ta kashe mafi karancin kudi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng