"Gidaje 3 na Mallaka": Buhari Ya Fadi Inda Yake Samun Kudi bayan Sauka daga Mulki

"Gidaje 3 na Mallaka": Buhari Ya Fadi Inda Yake Samun Kudi bayan Sauka daga Mulki

  • Muhammadu Buhari ya ce yanzu yana cin abinci da kuɗin hayar ɗaya daga gidajensa biyu na Kaduna, kuma bai tara dukiyar haram ba
  • Tsohon shugaban kasar ya ce Najeriya ƙasa ce mai wahalar shugabanci, inda ya ƙarfafa shugabanni su kasance masu adalci
  • Wannan na zuwa ne yayin da Gwamna Dikko Radda ya yi kira ga 'yan jihar Katsina da su zabi APC a zaɓen ciyamomin jihar mai zuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce yanzu yana samun kudin abinci ne idan ya karbi kudin hayar ɗaya daga gidajensa da ke Kaduna.

Buhari ya dage kan cewa bai tara dukiyar haram ba a lokacin mulkinsa, kuma ya jaddada muhimmancin gaskiya da rikon amana ga shugabannin Najeriya.

Muhammadu Buhari ya yi magana kan hanyar da yake samun kudaden kashewa
Buhari ya ce bai saci kudin talakawa ba, yayin da ya fadi hanyar da yake samun kudin cefane. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Buhari ya magantu kan wahalar shugabanci

Kara karanta wannan

'Na samu lafiya,' Buhari ya fadi kalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan bayanin ne yayin ganawa da shugabannin APC a Katsina, gabanin zaɓen kananan hukumomin jihar, inji rahoton This Day.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya ce Najeriya ƙasa ce mai wahalar mulki saboda yawan matsalolinta, inda ya ƙarfafa shugabanni su kasance masu riko da gaskiya da adalci.

Buhari ya ce:

"Najeriya ƙasa ce mai wahalar shugabanci, amma yawancin ‘yan Najeriya ba su gane haka ba sai sun samu mukamin shugabanci."

Ya ce ya fi jin daɗi da kuma samun lafiya a yanzu fiye da lokacin da yake shugabancin ƙasar, kuma mutane suna yabawa da canjin lafiyarsa.

Inda Buhari yake samun kudinn sayen abinci

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa bai saci dukiyar ƙasa ba a tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulki a matsayin shugaba.

Muhammadu Buhari ya kara da cewa babu wanda zai iya fitowa ya zarge shi da tara dukiyar haram a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi ɓaram ɓarama a siyasar APC, ya saki layi a gaban Ganduje

Ya ce yana da gidaje uku kawai, ɗaya a Daura da kuma biyu a Kaduna, kuma yana samun kuɗin haya daga ɗaya don gudanar da rayuwarsa.

“Bayan na yi shekaru takwas a matsayin shugaban kasa, gidaje uku ne kawai na mallaka; daya a Daura biyu kuma a Kaduna. Na sanya 'yan haya a cikin daya, inda nake samun kudin sayen abinci."

- Muhammadu Buhari.

Radda ya nemi a zabi 'yan takarar APC

Buhari ya ce akwai bukatar shugabanin Najeriya su kasance masu gaskiya da rikon amana yayin da suke rike da madafun iko.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya yi kira ga shugabannin APC su wayar da kan jama'a domin zaɓen ƙananan hukumomi.

Radda ya buƙaci shugabannin jam'iyya su nemi goyon bayan jama'a a yankunansu domin samun nasara a zaɓe mai zuwa.

Ya jaddada muhimmancin samun nasara mai cike da sahihancin kuri’u tare da tabbatar da ingantaccen tsarin zaɓe.

Kara karanta wannan

'Buhari ya nuna rashin gamsuwa da mulkin Bola Tinubu,' PDP ta tono magana

Ganduje ya kaddamar da yakin zabe a Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da yakin neman zaben jam'iyyar a jihar Katsina.

Kaddamar da yakin neman zaben na zuwa ne yayin da hukumar zaben Katsina ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a watan Fabrairu.

A wajen taron, sama da mutane 40,000 daga jam'iyyun adawa ne suka sauya sheka zuwa APC ciki har da tsohon shugaban PDP na jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.