'Harin Karya a Kano': Kwankwaso Ya Ragargaji 'Yan Sanda da Tinubu
- Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya taya mabiya Darikar Tijjaniyya murnar gudanar da Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass
- Rabi'u Kwankwaso ya nuna damuwa kan gargadin ‘yan sanda na yiwuwar hare-hare wanda ya haifar da tsoro ga al’umma da kuma mahalarta taron
- Sanata Kwankwaso ya yi kira ga ‘yan sanda su rika aiki bisa kwarewa kuma kada su kasance masu nuna bambancin siyasa a harkokinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya taya mabiya Darikar Tijjaniyya murnar kammala Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass da aka gudanar a Kano.
Kwankwaso ya bayyana gagarumin taron a matsayin alama ta hadin kai da zaman lafiya, wanda ya ja hankalin mutane daga cikin gida da kasashen waje.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan zargin siyasantar da tsaron jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magana kan maulidin Kano na 2025
Mabiya Darikar Tijjaniyya daga sassan duniya sun hallara a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano domin gudanar da Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass.
Wannan babban taro ya samu jagorancin Khalifan Tijjaniyya, Muhammad Sanusi II, da kuma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabi'u Musa Kwankwaso ya taya dukkan mahalarta taron murna kan nasarar gudanar da gagarumin bikin.
Kwankwaso ya ce taron ya tabbatar da karfin hadin kan mabiya Tijjaniyya a Najeriya da ma duniya baki daya.
Kano: Kwankwaso ya soki gargadin tsaro
Sai dai Sanata Kwankwaso ya bayyana damuwa kan gargadin hare-hare da ‘yan sanda suka fitar a daidai lokacin da ake shirin gudanar da Mauludin.
A cewarsa, wannan gargadi ya haifar da tsoro a tsakanin al’ummar Kano da baki daga sauran sassan Najeriya da kasashen waje, kuma aka gano ba na gaskiya ba ne.
“Gargadin ya nuna gazawar da ke tattare da yadda ‘yan sanda ke kula da harkokin tsaro.
Abin da ya faru zai iya sa mutane su daina daukar irin wannan gargadi da muhimmanci a nan gaba idan har akwai barazana ta gaskiya,”
- Rabi'u Musa Kwankwaso
Kiran da Kwankwaso gwamnatin tarayya
Kwankwaso ya bukaci ‘yan sanda su daina tsoma kansu cikin harkokin siyasar jihar Kano da sauran wurare.
Ya ce yana da muhimmanci su rika aiki bisa kwarewa da gaskiya domin dawo da martabar hukumar tsaro a idon duniya.
Haka zalika, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kada ta ci gaba da tsoma hannu a al’amuran da suka shafi ikon mallakar gwamnatin jihar Kano.
Ya bayyana cewa wannan rashin tsoma bakin zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban jihar.
Kalubale kan tsare-tsaren tsaro
Kwankwaso ya yi gargadi cewa irin wannan gargadi na karya daga bangaren ‘yan sanda zai iya haifar da matsala mai tsanani a nan gaba.
Ya bayyana cewa idan al’umma suka daina daukar irin wannan lamari da muhimmanci za a samu matsala idan aka samu barazanar tsaro ta gaskiya.
Ya kuma nuna damuwa cewa wannan hali zai iya rage kimar Najeriya a idon duniya, musamman ma yayin da aka sami mahalarta daga kasashen waje a irin wannan taro mai muhimmanci.
Jawabin Abba wajen maulidin Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi fatan alheri ga wadanda suka zo maulidin 2025 jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin jawabi wajen maulidin, ya kuma yaba da kokarin mai martaba Muhammadu Sanusi II wajen jagorantar taron.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng