Duk da Kokarin Abba, UNICEF Ta Gano Daliban Firamare na Kano ba Su Iya Karatu ba

Duk da Kokarin Abba, UNICEF Ta Gano Daliban Firamare na Kano ba Su Iya Karatu ba

  • Asusun UNICEF ya ce kashi 9.6% na yaran firamare a Kano ne kawai suka iya karatu, yayin da kashi 11.2% ne kacal suka iya lissafi
  • Shugabar UNICEF ta Kano, Rahama Mohammed ce ta bayyana hakan yayin taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya
  • Rahama ta yi bayanin yadda UNICEF ta horar da malamai da kuma samar da tsarin karatu na zamani ga yara masu karatun Islamiyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Asusun kula da kananan yara na UNICEF ya ce kashi 9.6% na daliban makarantun firamare na jihar Kano ne kawai suka iya karatu.

Da take jawabi a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025, shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Mohammed, ta ce kashi 11.2% ne kawai na daliban suka iya lissafi.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

UNICEF ta yi magana kan yaran da ba su iya karatu ba a jihar Kano
UNICEF ta ce kashi 9.6% na yaran jihar Kano ne suka iya karatun zamani da kyau. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

UNICEF ta gano daliban Kano ba su iya karatu ba

The Cable ta rahoto Rahama ta na cewa kimanin yara miliyan daya ne ba sa zuwa makaranta a Kano, kuma kashi 32% 'yan firamare ne, kamar yadda rahoton MICS na 2021 ya nuna masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahama Mohammed ta kara da cewa yankin Arewa maso Yamma, ciki har da Kano, Jigawa da Katsina, na da adadi mafi yawa na yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ta bayyana cewa yankin yana da kashi 16% na yara miliyan 10.2 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, inda Katsina kadai ke da fiye da yara 536,000.

"Daliban islamiyya na karatun zamani" - UNICEF

Rahama ta ce, saboda muhimmancin ilimi a matsayin hakkin dan Adam da kuma jagora na ci gaban al’umma, UNICEF ta gudanar da shirye-shirye daban-daban.

Wadannan shirye-shirye sun hada da tsara tsarin karatu na zamani da kuma koyarwa na Islamiyya, da horas da malamai sama da 290 da ma shugabannin makarantu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Ta ce tsarin karatun da UNICEF ta kaddamar ya tabbatar da cewa yaran da ke karatun Islamiyya suna samun ilimin zamani tare da karatun addini.

Dalibai 39,432 na cin gajiyar shirin WASH

Shugabar ta ce UNICEF na ci gaba da inganta gine-ginen makarantu tare da mayar da hankali kan kariya daga sauyin yanayi da samar da wuraren tsabta na shirin WASH.

Rahama ta bayyana cewa makarantu 33 a Kano da Jigawa suna cin gajiyar wannan shiri na WASH da ke amfanar yara 39,432.

Ta ce UNICEF ta mayar da hankali kan horas da malamai, inda malamai 1,109 suka samu horo kan yadda za su koyar da yara kanana da aiwatar da shirin RANA.

UNICEF ta samar da manhajar karatu kyauta

Hakazalika, UNICEF ta samar da fasahar zamani ta "Nigeria Learning Passport," a matsayin wani dandamali da yara za su koyi darussa fiye da 15,000 a kyauta.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasar Najeriya ya shirya ritaya, zai koma malamin makaranta

Rahama Mohammed ta ce kimanin yara, malamai, da iyaye 182,170 ne suka yi rijista da wannan dandamali na karatu na zamani.

Ta jaddada kudurin UNICEF na aiki tare da Kano, Jigawa, da Katsina domin magance matsalar ilimi tare da samar wa yara kyakkyawar makoma.

Abba ya gwangwaje daliban jihar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta raba kayan makaranta kyauta ga dalibai 789,000 a makarantu 7,092 don inganta karatun yara a jihar.

Gwamna Abba Yusuf ya ce wannan shiri zai taimaka rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta tare da tallafa wa iyayen marasa karfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.