Bayan Kokarin Titsiye Shi kan Badakalar $2.3bn na Kwangila, Buhari Ya Dawo Najeriya
- Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kammala ziyarar da ya kai a birnin Paris na kasar Faransa da ke Nahiyar Turai
- Buhari ya dawo gida Najeriya bayan kare martabar kasa a gaban Kotun Kasuwanci ta Duniya (ICC) a birnin Paris kan zargin badakalar $2.3bn
- Dattijon ya wakilci Najeriya ne kan shari'ar dala biliyan 2.3 da kamfanin Sunrise Power ya shigar a kotu, yana neman yin adalci
- Tsohon shugaban kasar ya bayyana jajircewarsa wajen kare muradun Najeriya a wannan muhimmin rikicin na duniya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya dawo gida Najeriya bayan ziyara a Paris kan shari'ar da aka shigar game da kwangilar Mambilla.
Buhari ya dawo da gida ne bayan kare martabar kasa a gaban Kotun Kasuwanci ta Duniya (ICC) da ke birnin Paris da ke Faransa.

Source: Twitter
Badakalar $2.3bn: Buhari da Obasanjo sun je Faransa
Tsohon hadiminsa bangaren sadarwa, Bashir Ahmad shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 24 ga watan Janairun 2025 a shafinsa na X.
Wannan na zuwa ne bayan rigimar kwangilar Mambilla tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin Sunrise Power ya kai gaban kotu kasuwanci da ke Faransa.
An tabbatar Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo sun isa Faransa domin su ba da shaida a gaban kotun kan shari'ar da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu.
Dukkanin tsofaffin shugabannin ƙasan guda biyu sun bar Najeriya domin zuwa ba da shaida a shari'ar kwangilar Mambilla ta neman diyya da kamfanin yake yi.
Buhari ya dawo Najeriya bayan kare kansa
Bashir ya wallafa wani faifan bidiyo yayin da Buhari ke sauka daga jirgin sama bayan isowa Najeriya a yau Juma'a 24 ga watan Janairun 2025.
Buhari ya wakilci Najeriya kan rikicin shari'ar dala biliyan 2.3 da kamfanin Sunrise Power ya shigar domin neman a yi adalci kan zargin badakala a lamarin.
Kamfanin yana korafi ne tare da neman adalci kan zargin badakalar kwangilar wutan lantarki ta Mambila.
Buhari ya kare martabar Najeriya a idon duniya
Tsohon shugaban kasar ya nuna jajircewa wajen kare muradun Najeriya, yana tabbatar da cewa ba za a bar martabar kasar ta zube ba.
"Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya dawo gida Najeriya bayan kare martabar kasar a gaban Kotun Kasuwanci ta Duniya (ICC) a birnin Paris dangane da shari'ar dala biliyan 2.3 da kamfanin Sunrise Power ya shigar."
- Cewar Bashir Ahmad
An bankado wasu bayanai kan badakalar $2.3bn
Kun ji cewa shugaban kamfanin Sunrise Power, Leno Adesanya, zai bayyana a gaban Kotun Kasuwanci ta Duniya (ICC) a Paris yau a shari'arsa da gwamnati.
Kamfanin, ta hannun lauyansa, Femi Falana SAN ya shigar da kara domin neman gwamnatin Najeriya ta biya shi Dala biliyan 2.3 saboda wasu dalilai.
Kamfanin Sunrise ya fara shari’a da gwamnati a 2017, yana neman diyya saboda zargin karya yarjejeniya a aikin tashar wutar lantarki ta Mambilla.
Asali: Legit.ng

