Hajjin 2025: Gwamnati Za Ta ba Alhazai Kyautar Kudi, an Ji Nawa Maniyyaci Zai Samu
- Maniyyatan Najeriya za su karbi tallafin BTA na $500, daidai da N830,000 bisa farashin musayar kudi na N1,660 kan kowace $1
- Farfesa Abdullahi Usman ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokarin ganin cewa alhazan 2025 sun samu saukin kudin kujera
- Hukumar NAHCON ta kuma yi bayanin abin da ya jawo maniyyata Hajjin 2024 ba su samu cikakken tallafin gwamnati na BTA ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Maniyyatan Najeriya da ke shirin zuwa aikin Hajjin bana a Saudiyya za su samu tallafin tafiye-tafiye (BTA) na $500.
Shugaban hukumar alhazan Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

Asali: Facebook
Maniyyata za su samu tallafin $500
Adadin kudin tallafin yana daidai da Naira 830,000, bisa sabon farashin musayar kudi na N1,660 kan $1 da aka samu a ranar Alhamis, inji rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NAHCON ta sanar da cewa N8,327,125.59 shi ne kudin kujerar aikin Hajjin 2025 ga maniyyata daga yankin Adamawa/Borno, wanda ya hada da jihohin Adamawa, Borno, Taraba da Yobe.
Ga sauran jihohin Arewa 14, kudin zuwa aikin Hajji ya kama N8,457,685.59, yayin da maniyyatan daga Kudancin Najeriya za su biya N8,784,085.59.
Hukumar ta bayyana cewa an tsayar da kudin aikin Hajjin ne a haka bayan tattaunawa tsakaninta da fadar shugaban kasa da shugabannin hukumomin maniyyata na jihohi.
Akwai yiwuwar samun saukin kudin Hajji
Farfesa Usman ya ce akwai yiwuwar a samu saukin farashin kudin kujerar idan gwamnati ta amince da biyan wasu kudaden tallafi da ake jira daga gare ta.
A wata hira da aka yi da shi a jaridar DCL Hausa, Farfesa Usman ya tabbatar da cewa maniyyata za su samu tallafin BTA na $500 kamar yadda aka tsara.
Ya ce rashin samun tallafin BTA da yawancin maniyyatan 2024 suka fuskanta ya faru ne saboda matsala daga hukumomin jin dadin alhazai na jihohi.

Kara karanta wannan
An sanya lokacin da maniyyata za su kammala biyan kudin Hajjin 2025 a jihar Kwara
Matsalar da aka samu a Hajjin 2024
Farfesa Usman ya ce hukumomin jihohi sun kasa fitar da kudaden maniyyata a kan lokaci don a canza su zuwa dalar Amurka ta hanyar Babban Bankin Najeriya (CBN).
Ya kara da cewa NAHCON ta tura kudin BTA din ga jihohi tun farko, amma yawancin jihohin sun kasa canza kudin daga Naira zuwa Dala.
Ya ce hauhawar canjin kudi a bara ya yi tasiri kan biyan tallafin $500 da aka yi wa maniyyatan 2024 alkawari.
Farfesa Usman ya tabbatar da cewa aikin rarraba BTA na karkashin ikon hukumomin jin dadin maniyyata na jihohi, ba NAHCON ba.
An sanya lokacin kammala biyan kudin Hajji
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta gargadi maniyyata da su gaggauta kammala biyan kudin aikin Hajjin 2025 kafin wa’adin da aka kayyade.
NAHCON ta ayyana ranar 31 ga Janairun 2025 a matsayin wa’adi na karshe da maniyyata za su kammala biyan kudin tafiyarsu zuwa kasa mai tsarki.
Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya jaddada cewa wadanda ba su kammala biyan kudin kafin wannan wa’adin ba, ba za su yi Hajji ba.
Asali: Legit.ng