Najeriya Ta Zama Hedikwatar Masu 'Bleaching', Minista Ya Fadi Illoli, Ya Gargadi Mata
- Ministan Lafiya ya nuna damuwa kan yadda ake kara amfani da kayan gyaran fata, wanda ke haifar da matsalolin kiwon lafiya da ke barazana ga rayuka
- Bincike ya nuna cewa kashi 77 cikin 100 na mata ‘yan Najeriya suna amfani da kayan bleaching, wanda ya sanya kasar gaba a duniya wajen amfani da kayan
- Gwamnatin Tarayya ta samar da dokokin tsaro kan kayan gyaran fata, ciki har da haramta sinadarai masu cutarwa, da wayar da kan jama'a kan illolin 'bleaching'
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Karamin Ministan Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ya koka kan yawan masu 'bleaching' a Najeriya.
Dr. Iziaq Salako, ya bayyana damuwarsa kan yawaitar amfani da kayan 'bleaching' a Najeriya da sauran kasashen Afirka.

Asali: Facebook
Najeriya ta samar da tsare-tsare kan 'bleaching'
Punch ta ruwaito cewa karamin Ministan ya jaddada cewa akwai barazanar lafiya da hakan ke haifarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Salako ya ce duk da illolin da aka sani na amfani da kayan 'bleaching' irin su man shafawa, sabulu, da allurai, an fi amfani da su tsakanin mutanen da ba farar fata ba.
A yayin wani taron wayar da kai kan cire kayan 'bleaching' da aka gudanar a Gabon, ya ce amfani da kayayyakin ya fi yawa a Afirka, musamman tsakanin mata.
A jawabinsa, Salako ya ce Najeriya tana kokarin kaddamar da wata sabuwar dokar kula da kayan kwalliya domin tabbatar da inganci da tsaron kayan da ake amfani da su.
Ya kara da cewa maza ma suna amfani da kayan 'bleaching', sannan su kan matsa wa mata lamba kai tsaye ko a kaikaice domin gyara fatarsu, don haka ya bukaci a saka maza cikin wayar da kai.
Najeriya ta zama hedikwatar masu 'bleaching'
Bincike na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kashi 77 cikin 100 na mata ‘yan Najeriya suna amfani da kayan 'bleaching', wanda ya sanya kasar ta zama ta daya a duniya wajen yawaitar amfani da irin wadannan kayayyaki.
Salako ya jaddada cewa kayan 'bleaching' na dauke da sinadarai masu guba irin su mercury, hydroquinone, da sauran nau’in karafa masu illa kamar arsenic da cadmium.
Ya tabbatar da cewa wadanan sunadarai suna janyo cututtuka masu tsanani kamar kansa, cewar Premium Times.
Gwamnatin Tarayya tana aiki domin hana kayan da ke dauke da sinadarai masu illa, ta hanyar dokoki irin su “Cosmetic Products Regulations 2019” da kuma amfani da hukumar NAFDAC wajen tantance duk wani kayan da ake shigo da shi.
A karshe, an gudanar da shirye-shirye na wayar da kan jama’a, da kuma amfani da fasaha kamar “MedSafety app” domin karbar rahotanni kan illolin da ake samu.
An fasa aure saboda cikon mazaunai
Kun ji cewa wani ango ya kekashe kasa ya ce ya fasa auren masoyiyar da ya so yin rayuwa da ita saboda ya gano tana amfani da ciko a mazaunanta.
Tsawon lokacin da masoyan suka shafe, angon bai taba ankara da cewar masoyiyar ta sa na yin ciko ba sai da aka zo yin hotunan kafin aure.
Asali: Legit.ng