Ku Daina Yiwa ‘Ya’yanku ’Bleaching’, Shawarin Likitan Fata Ga 'Yan Najeriya

Ku Daina Yiwa ‘Ya’yanku ’Bleaching’, Shawarin Likitan Fata Ga 'Yan Najeriya

  • Likita ya gargadi iyaye da su kula da amfani mayukan sauya launin fata ga ‘ya’yansu kanana saboda matsaloli na lafiya
  • Likita ya ce, amfani da man sauya launin fata ka iya jawo babban tsaiko ga lafiyar fatar dan Adam matukar ba a kula ba
  • Hukumar NAFDAC ta sha yiwa ‘yan Najeriya gargadi game da amfani da mayukan ‘Bleaching’ a kasar

Jihar Enugu - Wani kwararren likitan fata a asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya da ke Enugu, Dr Uche Ojinmah ya gargadi iyaye da su daina kodarwa da sauya fatar ‘ya’yansu.

Dr Ojinmah ya yi wannan gargadin ne tare da bayyana kadan daga illolin da ke tattare da mayukan da ake amfani dasu wajen mai da fatar dan Adam fara, Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa, wannan dabi’a ta sauya launin fata tana da matukar hadari ga lafiyar fatan dan Adam, musamman kananan yara da basu san komai ba.

Kara karanta wannan

Nagode Mama: Aminu Adamu ya Bada Hakuri a Fili, Yayi Alkwari Zai Gyara Halinsa

Da yake zantawa da jaridar ta Punch, Dr Ojinmah ya ce sinadaran da ake amfani dasu wajen yin mayukan sauya launin fatan na iya lalata hanta da koda da kuma kawo farfashewar fatar da ma manyan kuraje masu diwa a jiki.

Ku daina yiwa yara bleaching, inji likitan fata
Ku Daina Yiwa ‘Ya’yanku ’Bleacing’, Shawarin Likitan Fata Ga 'Yan Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Illolin da ke tattare da yin ‘Bleaching’

Abu ne sananne, man sauya launin fata na da tarihin haifar kazuwa, kyasbi, fata ta yi tabbare-tabbare da ma dai matsanancin kaikayin jiki da ka iya jawo babbar matsala ga lafiyar fata.

A cewarsa:

“Sauya launin fatan yara daidai yake da fara gasa kodarsu tun suna kanana, ya danganta da sinadarin sauya launin da kuke amfani dasu.
“Tsawon lokacin da ka dauka kana amfani da abu, iya adadin illoli da zai baka. Idan yara suka fara sauya launi tun suna kanana da sinadaran da suka hada da ‘steroids’ ko ‘hydroquinone’ ko ma dai ‘mercury’, za su gamu da illolinsu da wuri.”

Kara karanta wannan

Turji: Jami’an Gwamnati Suna Mora daga Ta’addanci, Shiyasa Basu son Ganin Bayan shi

A cewarsa, hakan zai takura asalin kwayoyin halittar ‘melanocytes’ da ke samar da sinadarin kariya ga fata mai kama da fentin baki da aka fi sani da ‘melanin’, wanda rashinsa ka iya jawo cutar dajin fata saboda rana ta samu damar dukan fatar.

Ya kara da cewa:

“Wannan yasa wasu daga cikinmu da ke da cutar zabiya ke da adadi mai yawa na masu cutar dajin fata har sai idan suna amfani da abin da zai kare su daga hasken rana.”

Ojinmah ya kuma shaida cewa, likitan fata ne mutum na farko da ya kamata mutane suke tuntuba idan suka samu matsalar fata, gashi ko farce.

Ba wannan ne karon farko da ake yiwa ‘yan Najeriya gargadin amfani da man sauya launin fata ba, hukumar NAFDAC ta sha yin hakan a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel