Shugaban Sojoji Ya Tallata Shirin Sulhu da 'Yan Bindiga a Katsina, Gwamna Radda Ya Yi Martani

Shugaban Sojoji Ya Tallata Shirin Sulhu da 'Yan Bindiga a Katsina, Gwamna Radda Ya Yi Martani

  • Gwamnatin tarayya ta kawo shirin yin sulhu da 'ƴan bindiga domin samun tsaro a yankin Arewa maso Yamma
  • Ta buƙaci gwamnatin jihar Katsina da ta goyi sabon shirin wanda zai sanya ƴan bindiga su ajiye makamansu tare da sako mutanen da suka sace
  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa ba zai nemi ƴan bindiga domin su zo a yi sasanci da su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta goyi bayan sabon shirin sulhu da ƴan bindiga wanda aka sanyawa sunan “Operation Save Corridor North-West".

An kawo shirin ne domin ba ƴan bindigan da ke miƙa wuya damar ajiye makamansu tare da sakin dukkanin mutanen da suka sace.

Batun sulhu da 'yan bindiga ya je Katsina
Gwamnatin tarayya na son sulhu da 'yan bindiga Hoto: @HQNigerianArmy, @dikko_radda
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce babban kwamandan runduna ta 8 ta sojojin Najeriya da ke jihar Sokoto, Manjo-Janar Ebikunle Ademola-Ajose, ne ya yi wannan kira yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, a ranar Laraba a Katsina.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kashe farfesan jami'a a gidansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ya kai wa Gwamna Radda batun sulhu da ƴan bindiga

Ya ce, bayan ziyarar tantance ayyukan da yake yi a jihohin da ke ƙarƙashin kulawarsa, babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, ya umurce shi da ya tattauna da gwamnatin jihar kan wannan sabon shirin.

"Saboda wasu daga cikin ƴan bindigan sun bayyana cewa suna son sasanci. Magana ta gaskiya, ba mu cikin shirin sasanci da su kai tsaye."
“Amma idan ana ƙoƙarin magance wannan muguwar matsalar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, wannan shirin abu ne da ya kamata a duba.”
“Babban hafsan tsaro ya umurce ni da na sanar da ku cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da Operation Save Corridor North-West. Ya yi kama da irin wanda aka ƙaddamar a yankin Arewa maso Gabas.”

- Manjo-Janar Ebikunle Ademola-Ajose

Ademola-Ajose, wanda shi ne kwamandan rundunar Operation Fansan Yamma da ta ƙunshi jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara da Katsina, ya ƙara da cewa babban hafsan tsaro ya tuntuɓi jihohin huɗu kan yadda za su haɗa kai don nasarar shirin.

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

A cewarsa, wannan tsari zai ba da dama ga ƴan bindigan da ke son miƙa wuya su ajiye makamansu, su saki mutanen da suka kama, sannan su koma cikin al’umma su zauna lafiya.

Wane martani Gwamna Radda ya yi

A martaninsa, Malam Dikko Radda ya bayyana cewa gwamnati ta yi taron tsaro inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi yarjejeniyar zaman lafiya da ake yi a ƙaramar hukumar Batsari.

"Na sha faɗi cewa ba zan tattauna da ƴan bindiga ba. Ba zan roƙe su domin su zo su yi sasanci da ni ba."
"Amma idan suka miƙa wuya kuma suka ce suna son tattaunawa, gwamnatin jiha za ta saurare su kuma ta ba su duk goyon bayan da ya kamata domin rayuwarsu da ta dabbobinsu."
“Muna da niyyar yin hakan, amma dole ne mu yi la’akari da dukkanin ƙalubale da kuma fa’idoji da rashin amfanin hakan."
"Mutanenmu ne, an haife su a nan, ciki har da iyayensu da kakanninsu, amma sun zaɓi zama masu laifi. Idan suka zaɓi zama nagartattun mutane, a shirye muke mu karɓesu."

Kara karanta wannan

Ganduje ya tuna baya, ya fadi yadda ya hana 'yan bindiga zama a Kano

- Gwamna Dikko Umaru Radda

Mutane sun yi fatali da sulhu da ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu daga cikin mutanen jihar Katsina sun yi watsi da shirin gwamnati na tattaunawa da ƴan bindiga domi m cimma yarjejeniyar sulhu.

Sun bayyana cewa sulhun ba shi da amfani domin an yi a baya amma hakan bai hana ƴan bindigan sake komawa su ɗauki makamai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel